An yanke wa wanda ya kai hari birnin New York hukunci
An yanke wa mutumin da ya kai hari birnin New York a shekarar 2016 hukuncin daurin rai da rai bayan an kama shi da laifin tayar da bama-bamai da suka yi sanadiyar jikkata akalla mutum 30. Mutum mai suna Raimi dan asalin kasar Afghanistan ne, da ya zama dan Amurka ya shiga hannun jami’an tsaro […]

An yanke wa mutumin da ya kai hari birnin New York a shekarar 2016 hukuncin daurin rai da rai bayan an kama shi da laifin tayar da bama-bamai da suka yi sanadiyar jikkata akalla mutum 30.
Mutum mai suna Raimi dan asalin kasar Afghanistan ne, da ya zama dan Amurka ya shiga hannun jami’an tsaro ne bayan musayar wuta, sannan ya sanar da kotu cewa “Ba ya kin jinin kowa.” Kamar yadda BBC ya ruwaito.
Masu shigar da kara sun ce mutumin mai shekara 30 bai nuna nadamar aika-aikar da ya yi ba kuma yana kokarin shigar da wadansu fursunoni cikin kungiyar IS.
An samu Raimi, wanda ake wa lakabi da “Chelsea bomber’ da dukan laifuffuka takwas da masu shigar da kara suka gabatar a kotu.
Gwamnan Jihar New York Andrew Cuomo ya bayyana cewa “an yi adalci.”
Mahaifin Raimi ne ya kai kararsa wajen Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka, (FBI), inda ya kira shi dan ta’adda a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta NBC.
daurin da aka yi masa na tabbatar da cewa zai yi wuya a sake shi kafin shekarunsa a duniya su kare.