An yanke wa ’yan daba 106 hukunci a kwana 10 a Kano
An yanke wa ’yan daba 106 hukunci ba tare da zabin biyan tara ba a kwanaki 10 Jihar Kano
A cikin kwanaki 10 kotu ta yanke wa ’yan daba 106 hukunci ba tare da zabin biyan tara ba a Jihar Kano.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar cewa a cikin kwanaki goman, kotu ta kuma ba da umarnin tsare karin wasu ’yan daba 43 a gidajen kangararrun yara.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa laifukan da kotu ta kama ’yan daban da su sun hada da kisa, fashi da makami, raunata jama’a da kuma sace mutane.
Kiyawa ya bayyana cewa wannan ya faru ne a cikin kwanaki 10, daga 24 ga watan Yuni zuwa 4 ga Yuli, 2024.
- Kotu ta tura tsohon ministan lantarki zuwa gidan yari
- Za a ci gaba da shari’a ba sai Ganduje ya halarci zaman kotu ba — Alƙali
Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya yana wa bangaren shari’a bisa rawar da ya taka wajen samun wannan nasara.
Sannan ya yi kira ga al’umma da su rika ba wa ’yan sanda hadin kai da bayanai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Jihar Kano.