An yanke wa ‘yan fashi uku hukuncin kisa
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke Dogarawa a Sabon Garin Zariya ta yanke hukuncin kisa ga mutum uku ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin aikata fashi da makami. Mutanen su ne Jimoh Abdullahi da Ali Abdullahi da Na- Malama, kuma duka suna zaune ne a Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna. Da […]
Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jihar Kaduna
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke Dogarawa a Sabon Garin Zariya ta yanke hukuncin kisa ga mutum uku ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin aikata fashi da makami.
Mutanen su ne Jimoh Abdullahi da Ali Abdullahi da Na- Malama, kuma duka suna zaune ne a Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Mai shari’a Mannir Muhammad Ladan ya bayyana hukuncin da aka yanke musu bisa laifin hada baki da fashi da makami wanda aikata hakan ya saba wa sashi na 97 PC da sashi na 6 (B) da kuma dokar Gwamnatin Tarayya ta shekara 2005, da ta tanadi hukuncin kisa ga wanda ya aikata fashi da makami.
An fara shari’ar ce a shekarar 2017 inda sai a ranar Alhamis din makon jiya 5/03/2020 aka kammala ta.
Wadansu mazauna garin Sabon Gari da suka halarci ganin yadda hukuncin zai kaya sun nuna gamsuwarsu da hukuncin da kotun ta yi, tare da kira ga gwamnati ta gaggauta tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke domin ya zama darasi ga wadanda suke addabar al’umma da fashi ko ayyukan ta’addanci.