An yanke wutar lantarkin gidan Firayiministan Pakistan

Hukumar wutar lantarki ta Pakistan ta yanke wa Firaministan kasar wuta, saboda ya ki biyan kudi. Wannan yankan wutar ya hada ginin majlaisar, har ma da wani yanki na gidan shugaban kasar, kmar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.Ministan ruwa da makamashi, Abid Sher Ali ya bayyana cewa, “ana yankar wuta babu kakkautawa,” […]

An yanke wutar lantarkin gidan Firayiministan Pakistan
An yanke wutar lantarkin gidan Firayiministan Pakistan

Hukumar wutar lantarki ta Pakistan ta yanke wa Firaministan kasar wuta, saboda ya ki biyan kudi. Wannan yankan wutar ya hada ginin majlaisar, har ma da wani yanki na gidan shugaban kasar, kmar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
Ministan ruwa da makamashi, Abid Sher Ali ya bayyana cewa, “ana yankar wuta babu kakkautawa,” don kwato basussukan kudin wutar lantarki da ake bi, kuma ya yi gargadin cewa duk wanda ya ki biya za a yanke masa wuta.
“Na bayar da umarnin yanke wuta a gidan saukar baki na majalisa da majalisar kanta da sakatariyar ofishin shugaban kasa, saboda sun ki biyan miliyoyin rupees da ake binsu na lantarki,” inji shi.
Hukumar Raya Birnin Islamabad, wadda ke da alhakin biyan kudin wutar lantarkin ofisoshin gwamnati, ta tara wa kanta dimbin bashi da Hukumar wuta ta IESCO ke binta, da ya kai Rupees biliyan biyu da miliya 360.
A halin yanzu, al’ummar kasar Pakistan na fama da karancin wutar lantarki da ya kai na kimanin sa’o’I 12 zuwa 18.