An yi addu’o’in cikar Alhaji Ibrahim Dasuki shekara 91

’Yan uwa da abokan arziki sun halarci gidan Sarkin Musulmi na 18, Alhaji Ibrahim Dasuki da ke titin Kabir a garin Kaduna domin yin addu’o’in cikarsa shekara 91 a duniya. Sai dai Alhaji Ibrahim Dasuki yana Ingila inda ake duba lafiyarsa, a lokacin da aka gudanar da addu’o’in. A sakonsa wanda tsohon Sarkin Gwandu Alhaji […]

An yi addu’o’in cikar Alhaji Ibrahim Dasuki shekara 91
An yi addu’o’in cikar Alhaji Ibrahim Dasuki shekara 91

’Yan uwa da abokan arziki sun halarci gidan Sarkin Musulmi na 18, Alhaji Ibrahim Dasuki da ke titin Kabir a garin Kaduna domin yin addu’o’in cikarsa shekara 91 a duniya.

Sai dai Alhaji Ibrahim Dasuki yana Ingila inda ake duba lafiyarsa, a lokacin da aka gudanar da addu’o’in. A sakonsa wanda tsohon Sarkin Gwandu Alhaji Mustapha Haruna Jokolo ya gabatar ya ce: “Ina goyon bayan a zabi duk wanda zai yi wa kasa aiki ba wanda zai jawo mata ci baya ba. Don haka nake shawarta jama’a su zabi na kwarai don dan Najeriya ne kadai zai iya gyara kasar nan, ba masu son kansu ba, ya dace a lura a gudu tare a tsira tare.” Ya ce a koyaushe yana tambayar masu zuwa gaishe shi a Ingila cewa, me ke faruwa a Najeriya, sannan yana yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, inda ya ce tashin hankali ba zai yi wa kowa alfanu ba. Wannan ne karo na 11 da ake gudanar da irin wannan addu’o’in. Da yake tofa albarakcin bakinsa bayan addu’o’in Alhaji Mamman Daura ya hori na baya su yi koyi da halin Alhaji Ibrahim Dasuki don mutum ne mai kula da cika alkawari da aiki tukuru da taimakon matalauta. Sanata Muhammadu Magoro ya ce Alhaji Ibrahim Dasuki mutum ne mai son jama’a, kuma ba ya nuna bambanci a tsakanin masu hali da matalauta. Taron addu’o’in ya samu halartar manyan mutane da suka hada da Alhaji Mustapha Haruna Jokolo da Alhaji Mamman Daura da Sanata Muhammadu Magoro da Alhaji Mu’azu Alhaji da Injiniya Buhari Bello da sauran dangi.
Limamin masallacin Sarkin Musulmi Bello, Sheikh Balele Wali da na masallacin Titin Yahaya, Imam Hassan Muhammad ne suka jagoranci adu’o’in.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista