An yi Allah wadai da yanke hukuncin kisa ga mutane 528 a Masar

Ana ci gaba da yin Allah wadai da wani hukuncin da wata kotu a Masar inda ta yanke wa mutane 528 magoya bayan Muhammad Morsi hukuncin kisa, sakamakon hannu da suke daga shi a kisan wani dan sanda.Majalisar dinkin Duniya da kungiyoyin kare Hakkin dan Adam da kasar Amurka da kuma Tarayyar Turai duk sun […]

An yi Allah wadai da yanke hukuncin kisa ga mutane 528 a Masar

Ana ci gaba da yin Allah wadai da wani hukuncin da wata kotu a Masar inda ta yanke wa mutane 528 magoya bayan Muhammad Morsi hukuncin kisa, sakamakon hannu da suke daga shi a kisan wani dan sanda.
Majalisar dinkin Duniya da kungiyoyin kare Hakkin dan Adam da kasar Amurka da kuma Tarayyar Turai duk sun bayyana damuwarsu da wannan hukuncin, inda suka jefa shakku kan ko kotun ta yanke hukuncin cikin adalci ganin  cewa ta yanke wannan hukuncin ne cikin kwanki biyu kawai na zaman ta.
Wannan ne hukunci kisa wanda ya kunshi mutane masu yawa da aka taba gani a tarihin kasar. Kuma hakan na nuni da yadda Gwamnatin Sojin kasar ke ci gaba da murkushi magoya bayan kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi wanda gwamnatin ta ayyana da “kungiyar ‘yan ta’adda”
An zartar da hukuncin ne ranar Litinin da ta gabata a  kotun birnin Minya inda aka danganta mutanan 528 da kisan wani dan sanda da kuma tashe-tashen hankula da suke faruwa a cikin kasar tun bayan hanbarar da gwamnatin Muhammad Morsi a watan Julin bara.
A nata bangaren kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana hukuncin ne da wata manuniya da ke nuna yadda bangaren shari’ar kasar Misira yake cikin halin-ni‘yasu.
Akwai kuma wasu mutane 683 ciki har da Shugaban kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi Muhammad Badie da kuma Shugaban Jam’iyyar ‘Yan Uwa Musulmi ta Freedom and Justice Party, wato Sa’ad al-Katatni da aka fara shari’arsu ranar Talatar da ta gabata.