An yi amfani da kwayoyi wajen lashe lambobi dubu 5 a gasar wasannin Olamfik daban-daban – Rahoto

Wani Bajamushe ya fitar da wani rahoto da ya girgiza duniya a jaridar Sunday Times ta Ingila a karshen makon jiya bayan ya tona irin tabargazarar da ta faru a wasannin Olamfik daban-daban a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2012. Rahoton da mutumin mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyo da talabijin mai suna ARD/WDR na […]

An yi amfani da kwayoyi wajen lashe lambobi dubu 5 a gasar wasannin Olamfik daban-daban – Rahoto
An yi amfani da kwayoyi wajen lashe lambobi dubu 5 a gasar wasannin Olamfik daban-daban – Rahoto

Wani Bajamushe ya fitar da wani rahoto da ya girgiza duniya a jaridar Sunday Times ta Ingila a karshen makon jiya bayan ya tona irin tabargazarar da ta faru a wasannin Olamfik daban-daban a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2012. Rahoton da mutumin mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyo da talabijin mai suna ARD/WDR na Jamus ya fitar ya nuna akalla lambobin yabo irin su Zinare da na Tagulla da kuma na Azurfa dubu 5 ne aka gano sun yi amfani da kwayoyin sanya kuzari wajen lashe su ba tare da an gano su ba a gasar Olamfik daban-daban da aka yi a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2012.
Rahoton ya nuna yadda aka gudanar da gwaje-gwajen jini kimanin dubu 12 daga ’yan wasa dubu 5 da suka halarci wasannin na Olamfik a shekarun da ake magana.
Rahoton ya bayyana yadda aka gano ’yan wasan Birtaniya su bakwai da suka yi amfani da kwayoyin da ke sanya kuzari wajen lashe lambobin yabo 10 a gasar Olamfik da ta gudana a birnin Landan a shekarar 2012 ba tare da an dago su ba sai bayan da aka kammala gasar.  Sai dai rahoton ya wanke shahararrun ’yan tsere Mo Farah daga Birtaniya da kuma Usain Bolt na Jamaika daga zargin yin coge.
Bayanin wannan bincike dai an same shi ne daga ma’ajiyar hukumar shirya wasannin Olamfik ta duniya (IAAF) amma mai tonon sililin dan kasar Jamus sai dai ya yi dabarar samo bayanan kuma ya watsa wa duniya ba tare da sanin hukumar ba.  Yin haka ya yi matukar tayar wa hukumar hankali inda yanzu haka ta bazama don yin binciken yadda al’amarin ya faru.  Rahoton ya kara da cewa har yanzu hukumar ba ta dauki mataki a kan ’yan wasan da aka same su da laifin yin magudi wajen lashe lambonin yabon ba, sai dai akwai yiwuwar hukumar za ta dauki mataki a kansu nan gaba.
Shugaban Hukumar da ke yin gwajin jini ta duniya (World Anti-Doping Agency, WADA) Sa Craig Reedie ya nuna kaduwarsa a kan wannan bayani da dan jaridar ya bankado.  Ya ce ko shakka babu hukumarsa za ta cigaba da yin binciken kwakwaf a kan ’yan wasa a duk lokacin da za a yi wata gasa nan gaba, don gudun sake faruwar irin haka nan gaba.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja