An yi artabu tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar Iraki
Masu zanga-zanga a Iraki sun kara arangama da jami’an ‘yan sanda a binrin Baghdad, a daidai lokacin da suke cika shekara daya da zanga-zangar kin jinin gwamnati mai ci. A ranar Litinin ’yan sanda suka tarwata dubban masu zanga-zangar ta hanyar harba musu hayaki mai sa hawaye. #EndSARS: Farashin shinkafa ’yar waje ya fadi warwas ’Yan […]
A ranar Litinin ’yan sanda suka tarwata dubban masu zanga-zangar ta hanyar harba musu hayaki mai sa hawaye.
Bangarorin sun yi dauki ba dadi ne s daidai lokacin da masu zanga-zangar ke kona tayoyi da jefe-jefe a kan gadar Al-Jumhuriyah, da ake bi a tsallake kogin Tigris, zuwa yankin Green Zone.
Hanyar Green Zone na cike da matakan tsaro, kuma wuri ne mai ofisoshin jami’an gwamnati, da na jakadacin Amurka.
Idan ba a manta ba, masu zanga-zangar da suka gudanar a bara, sun mamaye manyan garuruwa da ke Kudanci Iraki inda mabiya akidar Shi’a ke da rinjaye.