An yi asarar rayuka da dukiya a harin bom na kasuwar Bauchi

A marecen Litinin da ta gabata, wasu tagwayen bama-bamai suka tashi a cikin Kasuwar Santaral da ke kusa da gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin, Sheikh dahiru Usman Bauchi, inda shaguna da dama suka kone kurmus tare da asarar rayuka da dimbin dukiyoyi.Bayan faruwar lamarin, da yawa daga cikin mutanen fadin jihar sun shiga cikin mawuyacin […]

An yi asarar rayuka da dukiya a harin bom na kasuwar Bauchi
An yi asarar rayuka da dukiya a harin bom na kasuwar Bauchi

A marecen Litinin da ta gabata, wasu tagwayen bama-bamai suka tashi a cikin Kasuwar Santaral da ke kusa da gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin, Sheikh dahiru Usman Bauchi, inda shaguna da dama suka kone kurmus tare da asarar rayuka da dimbin dukiyoyi.
Bayan faruwar lamarin, da yawa daga cikin mutanen fadin jihar sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon fashewar.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi, DSP Haruna Muhammed ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai kuma bai bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin ba.
Wakilinmu ziyarci Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi, inda aka kai wadanda suka samu munanen raunuka.
Dokta Sa’idu Abubakar, shi ne shugaban riko na asibitin. Ya bayyana wa wakilinmu cewa mutum 8 ne suka rasa rayukansu, kana mutum 28 suna kwance a asibitin, inda ake ci gaba da duba lafiyarsu.
A wata takarda da ya raba wa manema labarai a Bauchi, jami’in yada labarai na Gwamna Isa Yuguda, Mista Ishola Adeyemi ya bayyana cewa gwamnan ya yi Allah wadai da harin, sannan ya ba da umurni ga Kwamishinan Lafiya, Dokta Sani Abubakar Malami, cewa a ci gaba da kula da wadanda harin ya rutsa da su. Sannan gwamnatin jiha ta dauki nauyin biyan kudin magunguna ga marasa lafiyar.
Alhaji Adamu Gajere, shi ne Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa ta Santaral. Ya bayyana wa manema labarai cewa an yi asarar sama Naira miliyan 150 a kasuwar. Ya yi roko ga gwamnatin jiha da ta kawo masu dauki.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista