An yi asarar sama da N300bn a zanga-zangar yunwa — Shettima

Shettima ya buƙaci yaran su kasance mutane na gari domin taimaka wa Najeriya.

An yi asarar sama da N300bn a zanga-zangar yunwa — Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya ce an yi asarar sama da Naira biliyan 300 sakamakon ɓarnar da aka yi a lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance.

Shettima, ya yi wannan jawabi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da ya gana da ƙananan yaran da Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sakin su.

Ya ce asarar da aka yi ta shafi shafar dukiyoyin ɗaiɗaikun mutane da kuma ’yan kasuwa.

Ya bayyana cewa, duk da shaidar da ake da ita a kan yaran da ake tuhuma, amma Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a sakin su saboda tausayi.

“Ko da yake akwai hujojji na bidiyo da hotuna na abin da ya faru—wasu matasan da kansu suka wallafa abin da suka aikata.

“Amma shugaban ƙasa, a matsayinsa na mai tausayi, ya ba su damar gyara halayensu don zama ’yan ƙasa na gari da za su taimaka wajen gina Najeriya,” in ji Shettima.

Ya shawarci yaran da kada su bari a yi amfani da su wajen haddasa tashin hankali ko lalata dukiyoyin jama’a.

Shettima, ya kuma buƙaci gwamnonin jihohi da sauran shugabanni da su taimaka wajen bai wa yaran horo da tarbiyya domin su zama ’yan ƙasa na gari.

“Na yi kira ga gwamnoninmu da wakilanmu su haɗa kai domin inganta Najeriya baki ɗaya, hakan ya fi komai muhimmanci duk da bambancin siyasa,” in ji shi.

“Mu dawo da waɗannan yaran cikin al’umma ne don taimakawa rayuwarsu.”