An yi bikin baje-kolin littattafan Musulunci dubu 5 a Abuja

A ranar Asabar  da ta gabata ce aka bude bikin baje-kolin  littattafan Musulunci fiye da dubu 5 a Abuja. Kamfanin De Minaret  International ne ya dauki nauyin shirya bikin a dakin taro da ke Babban Masallacin Juma’a na Abuja.Babban bako mai jawabi a wurin taron Farfesa Ibrahim Suleiman ya gabatar da lacca mai taken ‘Jahadin […]

An yi bikin baje-kolin littattafan Musulunci dubu 5 a Abuja
An yi bikin baje-kolin littattafan Musulunci dubu 5 a Abuja

Farfesa Ibrahim Suleiman (na biyu daga dama) da Shugaban De Minaret International Yusuf Sa’eed (na uku daga dama)da sauran jama’a yayin bude taron nuna littattafan Musulunci a AbujaA ranar Asabar  da ta gabata ce aka bude bikin baje-kolin  littattafan Musulunci fiye da dubu 5 a Abuja.
Kamfanin De Minaret  International ne ya dauki nauyin shirya bikin a dakin taro da ke Babban Masallacin Juma’a na Abuja.
Babban bako mai jawabi a wurin taron Farfesa Ibrahim Suleiman ya gabatar da lacca mai taken ‘Jahadin Usman danfodiyo: Ilimi ne jigo’, ya ce rayuwa ba za ta tafi cikin tsari ba sai da ilimi, ba za a samu ilimi ba sai an rika karance-karance.
Ya ce: “Lokacin da Shehu danfodiyo da mutanensa za su fara jihadi, sai suka fahimci babban makamin da za su rike yayin jihadi shi ne ilimi. Sun fahimci ba za a iya canza jama’a ba tare da an ba su ilimi ba. Hakan ya sanya suka mayar da hankali kan ilimi. danfodiyo ya rubuta littattafai fiye da 300, don haka ya kamata Musulmi su mayar da hankali wurin karance-karance, saboda sai da ilimi ne za su san Allah da kuma yadda za su bauta maSa.”
Ya ce babu babbar cuta a duniya da ta wuce jahilci, ko ciwo ne idan ba a san shi ba za a iya maganinsa ba.
Darakta a Cibiyar The Institute of Administration da ke Zariya, kuma lakcara a Tsangayar Koyar da Addinin Musulunci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Muhammad Bello Usman ya yi karin bayani a wurin taron ne ya ce tabbas sun fahimci babu abin da ya fi ilimi muhimmanci a rayuwar dan Adam, kuma kowane ilimin yana da amfani ga Musulmi.
“Kowane ilimi walau na addini ko na zaman duniya ko na sana’a duka na da muhimmanci a rayuwar  Musulmi.  Idan muka duba malaman addini irinsu Ibn Khaldun da Ar-Razi da Ibn Sinai da Abduljabbar dukkansu malamai ne kuma masana a bangaren shari’ar Musulunci da kimiyya da fasaha da lafiya da alkalanci da sauransu.”
 Wasu daga cikin littattafan da aka nuna a lokacin taronYa ce a da limami shi ne sarki kuma shi ne alkali, saboda yana da ilimi shari’a da na sallah da kuma na mulki. “Don haka ina fata kowane Musulmi zai nemi dukkan ilimi; na addini da na zamani. Dukkansu suna da amfani kuma halal ne Musulunci.” Inji shi.
“Dangane da wadanda suke cewa karatun boko haramun ne sai na ce sun yi gurguwar fahimta, kuma wannan batu da ake ta cece-kuce a kansa ma ai Turawa ne suke yada farfaganda a kansa, idan aka duba tarihi babu wani malamin addinin Musulunci da ya ce karatun boko haramun ne.”
Shugaban Kamfanin De Minaret International Dokta Saheed Abdur-Ra’uf a lokacin da yake jawabin maraba ne ya ce sun shirya bikin ne don bunkasa tare da cusa dabi’ar karatu a zukatan Musulmi.

“Mun shigo da littattafan Musulunci daga kasashen duniya sama da dubu 85, sannan muka saukar da farashinsu don Musulmi su samu damar karanta littattafan cikin sauki. Babban makasudin gudanar da wannan taron shi ne don mu bunkasa tare da cusa dabi’ar karatu a zukatan Musulmi, hakan zai ba su damar gudanar da rayuwarsu kamar yadda addini ya tanadar.”
Ya ce, yakan ji takaici idan ya tuna yadda duniyar Musulmi ta samu kanta, Musulmi sun samu kansu cikin kaskanci. “A da wadanda ba Musulmi idan za su yi yanka mu suke kira mu yi musu, komai nasu sai sun sanya mu a ciki, amma a yanzu ba mu da kima ko daraja a wurinsu, an nuna musu mu makiyansu ne, masu kashe su, kullum idan aka kai hari sai a ce Musulmi ne, an bar mu da kare kai da kuma magiya. Mun samu kanmu cikin wannan matsala ce sakamakon rashin karance-karancen littattafan Musulunci da kuma aiki da abin da muka  karanta.”
Ibrahim Hassan wanda ya halarci taron ya ce ya karu sosai, kuma hakan zai sa ya zage damtse wajen neman ilimi ba wai kawai a bangare daya ba.
Hajara Umar ta ce wannan taron da ta halarta ya zaburar da ita wajen fara karance-karance.
A yayin bikin an nuna littattafan da suka hada da: kur’ani da Hadisai da na shari’a da tarihi da na tattalin arzki da na siyasa da  na Fikhu da Tajawidi da koyar da aikin hajji da na yara  da sauransu.
A cikin littattafan akwai: ‘The Greatest Story of Holy kur’an’ da ‘Fifty Candles’ da ‘Saboir of Islamic Spirit” da ‘Man And Destiny’ da ‘The Lawful And Prohibition In Islam’ da ‘The End Of the World’ da ‘The Choice’ da ‘Islam and Christianity bol 1’ da ‘The Spritual Life’ da ‘Da’awah in Islam’ da ‘The Muslim Women: Her Beauty and Chastity’ da ‘Heaben Under Your Feet’ da ‘Drops From An Ocean’ da sauransu.
Littattafan yara sun hada da ‘Adbentures In Islam’ da ‘Trabellers From The Heaben’ da ‘Human Mobra’ da ‘The Story of a Beggar Boy’ da sauransu.
An saukar da farashin littatafan daga kashi 10 zuwa 65 cikin 100 na asalin farashinsu.
Za a rufe taron gobe Asabar idan Allah Ya kai mu.Wadansu mata suke duba littattafai yayin taron