An yi bikin kaddamar da kungiyar Alkalam a Kaduna

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da taron kaddamar da kungiyar Marubuta Alkalam (KMA) da kuma baje kolin littattafai a dakin taro na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).Babban bako mai jawabi a wurin taron, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya gabatar da jawabi mai taken ‘Bunkasar Harshen Hausa Da Barazanar Da Yake Fuskanta.’A […]

An yi bikin kaddamar da kungiyar Alkalam a Kaduna
An yi bikin kaddamar da kungiyar Alkalam a Kaduna

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da taron kaddamar da kungiyar Marubuta Alkalam (KMA) da kuma baje kolin littattafai a dakin taro na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).
Babban bako mai jawabi a wurin taron, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya gabatar da jawabi mai taken ‘Bunkasar Harshen Hausa Da Barazanar Da Yake Fuskanta.’
A jawabin nasa, ya ce: “Bunkasuwar kowane harshe ta ta’allaka ne da ire-iren yadda masu shi da masu sha’awarsa da manazartansa suka tsaya kai-da-fata don ganin ci gabansa ta hanyar yin rubuce-rubuce da bincike-bincike da kuma yada shi a duniya”
Ya ce babu wani harshe da zai ci gaba ko ya bunkasa, idan har babu rubuce-rubuce ko kuma sadarwa ta hanyar magana da shi.
Shugabar kungiyar Alkalam, Hajiya Baida’u Muhammad Gada ta bayyana tarihin kungiyar, inda ta ce: “kungiyar kamar sauran irinta a wasu sassan kasar nan, wakiliya ce a inuwar Duniyar Marubuta, mai hedkwata a birnin Kano. Wacce ta kunshi dukkan kungiyoyin marubuta a nan cikin gida da kuma kasashe makwabta, inda ake magana da harshen Hausa.”
Ta ce an kafa kungiyar ne don bunkasa harshen Hausa a cikin shekarar 2003 da mambobi 10, wanda kuma a yanzu mambobinta za su kai akalla guda 100.
Sauran wadanda suka gabatar da jawabai sun hada da, Shugaban Tsangayar Nazarin Halittar dan Adam ta Jami’ar Jihar Kaduna, Dokta Yusuf Nadabo da tsohon dan jarida, Mahmoon Baba-Ahmed da Shugaban Gidan Rediyon Liberty, Dokta Tijjani Ramalan, wanda Usman Ahmad Kabara ya wakilta da Hajiya Amina Lamido da Kwamared Shehu Sani, wanda Malam Tanimu Ladan ya wakilta da Babban Sakatare a Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Kaduna,  Alhaji  Isa Sama’ila; wanda ya wakilci Gwamna Mukhtar Ramalan Yero na Jihar Kaduna  da Hakimin Kakuri Alhaji Shehu Tijjani da sauransu.
Daga bisani, an gabatar da lambobin girmamawa ga Malam Ado Ahmad Gidan Dabino da shahararren mawaki Aminu Ala da Mahmoon Baba-Ahmed da sauransu.
A lokacin kaddamar da kungiyar, Shugaban Gidan Rediyon Liberty, Dokta Tijjani Ramalan ya ba da gudunmuwar  Naira dubu 50, sai Editan Jaridar Blueprint, Ibrahim Sheme da mawaki Aminu Ala da Dokta Ahmad Inuwa, wanda Alhaji Sa’idu Gombe ya wakilta da kuma Hakimin Kakuri Alhaji Shehu Tijjani da suka ba da Naira dubu 20 kowannensu. Sai kuma dan Majalisa  Mustapha  Zigogi, wanda ya ba da Naira dubu 10.
Sauran wadanda suka samu halartar taron sun hada da Shugaban kungiyar Direbobin Sufuri ta kasa, (NURTW) reshen Unguwar Rimi Kaduna, Muhammad Sabitu danjinjiri da mawaka kamar su Abubakar Sanida Nasiru G. Ahmad da Nafi’u Salisu da Sa’adatu Sadik da sauransu.