An yi bikin nadin Shehun Bama cikin dokar hana fita

An yi bikin nadin sarautar Shehu Umar II Al-Amin El-Kanemi a matsayin Shehun Bama na biyu. Sarkin mai daraja ta daya zai jagoranci masarautar Bama da ke jihar Borno. An gudanar da bikin nadin sarautar gargajiyar ne a ranar Asabar 9 ga watan Mayu 2020 a fadar Shehun da ke garin Bama. Shehun Bama ya […]

An yi bikin nadin Shehun Bama cikin dokar hana fita

Shehun Bama, Alhaji Umar Ibn Kyari Umar El-kanemi

An yi bikin nadin sarautar Shehu Umar II Al-Amin El-Kanemi a matsayin Shehun Bama na biyu.

Sarkin mai daraja ta daya zai jagoranci masarautar Bama da ke jihar Borno.

An gudanar da bikin nadin sarautar gargajiyar ne a ranar Asabar 9 ga watan Mayu 2020 a fadar Shehun da ke garin Bama.

A dalilin dokar zaman gida da aka kakaba a jihar da nufin dakile yaduwar cutar coronavirus, bikin mika sandar mulki a hukumance zai gudana ne a wani lokaci nan gaba.

“Amma muna tabbatar muku cewa bikin mika sandar mulkin zai gudana bayan komai ya yi sauki inda za mu gayyaci ‘yan uwa da abokan arziki na cikin gida har da kasashen waje”, inji dan uwan sabon Sarkin, Abba Bukar Abba Masta, a wani bayanin da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“Muna kuma ba da hakuri a kan yadda muka gudanar da bikin ba tare da gayyatar jama’a sosai ba. Hakan ya faru ne saboda ganin halin da ake ciki”.

A ranar 4 ga watan Mayu ne gwamnan jihar, Babagana Zulum, ya sanar da mika ragamar sarautar ga Shehu Umar II, a matsayin sabon Shehun bayan rasuwar mahaifinsa Shehu Kyari Umar Ibn Ibrahim Al-Amin El-Kanemi a ranar 27 ga watan Afrilu.