An yi bikin radin sunan ‘yar baiwa a Kano

Fiye da mutane 100 ne wadanda suka hada da ’yan uwa da abokan arziki da ma’aikatan Babban Asibitin Gwarzo suka taru a ranar Larabar da ta gabata a harabar asibitin, don bikin sunan jaririya yar baiwa da aka haifa makonni biyu da suka gabata, wacce aka haifa a wajen mahaifa.Bayan an gabatar da addu’a kamar […]

An yi bikin radin sunan ‘yar baiwa a Kano

Maijego a tsakiya tare da mahaifiyarta da jaririyar da ta haifaFiye da mutane 100 ne wadanda suka hada da ’yan uwa da abokan arziki da ma’aikatan Babban Asibitin Gwarzo suka taru a ranar Larabar da ta gabata a harabar asibitin, don bikin sunan jaririya yar baiwa da aka haifa makonni biyu da suka gabata, wacce aka haifa a wajen mahaifa.
Bayan an gabatar da addu’a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sai aka sanya wa yarinyar suna A’isha. Sannan aka rarraba abin taba ka lashe ga duk daukacin mutanen da suka halarci radin sunan, abincin da ma’aikatan asibitin ne suka daukin nauyin bayarwa. Baya ga wannan kuma suka bayar da kyautar zannuwa ga maijego da kuma riguna ga jarriya Aisha.
Aminiya ta rawaito cewa dukkanin ma’aikatan asibitin tun daga kan Shugaban asibitin har zuwa kan maigadi babu wnada bai halarci rasdin sunan na “’yar baiwa” ba
Ma’aikatan asibitin sun bayyana cewa an yi wannan bikin suna ne a harabar asibitin kasancewar a cewarsu wannan haihuwa ita ce irinta ta farko, sannan kuma kasancewar mai jegon har yanzu tana kwance a asibitin.
Mahaifin jaririyar, Muhamad Lawal ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa wannan kyauta da ya yi musu, tare da daukar alkawarin ilimantar da yarinyar don ta zama mai amfani ga al’umma.
Ita ma kakar jaririyar wacce ta yi bayyani cikin zubar da hawaye ta zayyana godiyarta ga Allah bisa wannan haihuwar baiwa da ya nufi ‘yarta wacce ta ce ita ce babba a cikin ‘ya’yan da haifa.
A kwanakin baya ne mahaifiyar jaririyar mai suna Binta ta tafi asibitin Gwarzo wanda yake da nisan  kilomita 80 daga cikin birnin Kano, da tsohon cikinta wata tara, wanda daga bisani ya zama bakon abu a cikin litattafan aikin likita.
Bayan ta ga likita ne sai aka umarce ta da ta je ta yi hoto, saboda ana tunanin akwai wani abu wanda yake ba daidai ba ga juna biyun da take dauke da shi. Sai dai a yayin da sakamako ya fito inda likitoci suka daga hoton cikin nata sai suka yi arba da wani bakon abu, inda suka samu cewa ciki yakai watanni tara, sai dai ba a cikin mahaifa yake ba, yana dashe a tsakanin hanjinta da cikinta a wani wuri da ba shi da ruwa. Irin wannan cikin likitoci kan kira shi da cikin bayan mahaifa.
Sai dai abin da ya bai wa ma’aikatan asibitin mamaki shi ne, ganin yadda jarririyar ke raye a cikin kuma a shirye take da a haifo ta, wanda a cewarsu idan aka samu irin hakan da wuya a samu jaririn ya ci gaba da girma zuwa wata tara.
Likitoci sun bayyana cewa “babu yadda za a yi a haifi irin wannan jaririyar ta hanyar da aka saba, don haka dole sai dai a yi wa mahaifiyarta fida don fitar da jaririyar. Hakan ya sa washegari aka shiga da Binta dakin tiyata, inda Shuagaban Asibitin Dokta Charles Onyia ya jagoranci tawagar likitocin da suka yi mata tiyata, inda sukafitar da jaririyar daga cikin mahaifiyarta a cikin minti 30.   
 Dokta Onyia ya shaida wa Aminiya cewa “bayan wannan mata ta gwada maganin gargajiya  ba ta samu sa’a ba, sai ta zo asibitinmu, inda muka umarce ta ta yi hoto. Da na taba cikinta sai na ji wani abu a wajen mafitsararta” Inji shi.
Daga sakamakon da aka samu bayan ta yi hoto har zuwa aikin cire jaririyar da aka yi ya bude sabon shafi a rayuwar Dokta Onyia. “Zan iya tunawa a lokacin da nake dalibi a Jami’a kimani shekaru 20 da suka wuce Farfesa Orhue na Jami’ar Benin ya taba fadin cewa hakan ba zai taba faruwa ba, wato idan aka samu irin wanann cikin a wajen mahaifa ba zai yi girman da zai kai wata tara ba, idan kuma har ya kai to jaririn ba zai rayu ba. Ina alfaharin shaida maka cewa a duniyar nan ba mu taba ji, ko ganin inda aka haifi jaririn a raye ba. Abu ne da ba a fiye samu ba ko a cikin litattafai. Yawanci idan hakan  ta faru to jaririn da uwarsa sukan mutu ne a wajen fidar, don haka muke kiran wannan haihu da ta baiwa” Inji shi.
Hukumar asibitin ta bayyana cewa da mai jego da jaririyarta suna cikin koshin lafiya. Haka kuma jaririyar tana shan nono sosai.
Wata kwarariyar likitar mata a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Dokata Hauwa Musa Abdullahi ta tabbatar da cewa irin wannan haihuwa abu ne da ba a fiye samu ba, sai dai kuma abu ne da  zai iya yiwuwa.
Ta bayyana cewa akwai lokacin da suka samu irin wannan lamarin inda suka yi wa wata mata fida aka kuma sami jaririn a raye. Haka kuma  a kwanakin baya ta ce sun yi wa wata mata fida duk da cewa ba a samu jaririn a raye ba.
Dokata Hauwa ta bayyana cewa lamarin samun cikin a wajen mahaifa abubuwa da yawa ne ke kawo shi kamar daukar cuta da sauransu.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu