An yi bikin Ranar Ba-haya ta duniya a Abuja

Kungiyar masu gidajen wanka ta Abuja ta gudanar da bikin Ranar Ba-haya ta Duniya, inda ta bukaci ma’aikatar birnin ta ba da damar kafa wuraren ba-haya a wasu yankunan birnin don magance matsalar yin bayi a bainar jama’a da ke kawo kazanta. Kungiyar wadda ta bayyana haka jim kadan bayan tattaki na musamman a yayin […]

An yi bikin Ranar Ba-haya ta duniya a Abuja

Waxansu mambobin Qungiyar Masu Gida Wanka ta Abuja

Kungiyar masu gidajen wanka ta Abuja ta gudanar da bikin Ranar Ba-haya ta Duniya, inda ta bukaci ma’aikatar birnin ta ba da damar kafa wuraren ba-haya a wasu yankunan birnin don magance matsalar yin bayi a bainar jama’a da ke kawo kazanta.

Kungiyar wadda ta bayyana haka jim kadan bayan tattaki na musamman a yayin bikin Ranar Ba-haya ta Duniya da a ka yi a ranar Litinin da ta gabata, ta yi korafin cewa wurare da dama da mambobinta suka gina ba-haya, aikin rusa gine-gine ya rutsa da su a baya, har yanzu ba ta samu izinin sake mayar da su ba.

Mambobin da suka sanya suturun da suke dauke da bayanan fadakarwa, sun zaga wasu muhimman yankuna a birnin tare da yin lakcoci a wuraren da jama’a ke tsayawa da suka hada da Mahadar Bega da ta Eriya Wan, da kuma Tashar Mota ta Jabi.

A yayin lakcar wanda ya samu rakiyar ma’aikatan Hukumar Duba-Gari ta Abuja (A.E.P.B), an fadakar da jama’a a kan illolin yin ba-haya a fili da kuma irin matsalolin da hakan ke haddasawa a kan muhalli.

Kuma an gudanar da wani taro a babban zauren Cibiyar Al’adun Gargajiya ta Abuja wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnati daga bangaren hukumar birnin, inda Kodinetan Hukumar Kula da Birnin Abuja (A.M.M.C), Malam Umar Shu’aibu ya wakilci Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello.

A jawabin da ya gabatar, ya ce Ministan Abuja ya kafa kwani kwamiti don kawo karshen matsalar karancin wuraren ba-haya a wasu wurare na musamman inda nan ba da dadewa ba za a aiwatar da shawarwarin nasu da ya ce sun gabatar.

Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Ba-haya da Wanka ta Abuja, Alhaji Aminu Musa ya ce yanzu haka kungiyar tana gudanar da wuraren ba-haya sama da 200 da ta gina a yankunan kananan hukumomin Abuja 6, wadanda ya ce ta fara gudanarwa kamar shekara 20 a yanzu. Sauran bangarori da suka halarci taron sun hada da wakilai daga Ma’aikatar Kare Muhalli ta Tarayya da Ma’aikatar Ruwa da kuma wasu kungiyoyi da ke da nasaba da lamarin muhalli.