An yi bikin ranar masu harhada magunguna ta duniya

Ranar 25 ga Satumban da ya gabata ne aka ajiye a matsayin Ranar Masu Harhada Magunguna ta Duniya, inda qwararru da sauran masu ruwa-da-tsaki a fannin ke gangamin wayar da kan jama’a game da rawar da suke takawa wajen kiwon lafiyar dan Adam. An fara bukukuwan ranar ce a watan Satumbaa shekara ta 2010, bayan […]

An yi bikin ranar masu harhada magunguna ta duniya

Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole

Ranar 25 ga Satumban da ya gabata ne aka ajiye a matsayin Ranar Masu Harhada Magunguna ta Duniya, inda qwararru da sauran masu ruwa-da-tsaki a fannin ke gangamin wayar da kan jama’a game da rawar da suke takawa wajen kiwon lafiyar dan Adam.

An fara bukukuwan ranar ce a watan Satumbaa shekara ta 2010, bayan a shekara ta 2009 taron qoli na qungiyar masu harhada magunguna ta duniya, ‘International Pharmaceutical Federation ya amince da kebe ranar 25 ga Satumban kowace shekara domin gudanar da wannan gangami.

Haka kuma ranar ta yi daidai da ranar da aka kafa qungiyar a 1912 da hedkwata a qasar Netherlands wacce a yanzu kuma ke da fiye da mambobi miliyan daya a qasashe 139 na duniya.

Najeriya ta bi sahun qasashen duniya wajen gudanar da wannan gangami a karo na 9, inda wani masani, Bala Maikudi, Shugaban Qungiyar Masu Harhada Magunguna ta Najeriya reshen Jihar Kano ya fayyace abubuwan da suke muradin cimmawa kamar yadda wakiliyarmu ta ruwaito.

Bala Maikudi ya ce “Abin da muke so shi ne mutane su san wane ne mai hada magani kuma mene ne hada magani yake yi, sannan ina za ka samu mai hada magani kuma wace shawara za ka nema daga gare shi?”

“Dalilin wadannan tambayoyi kuwa shi ne yawan da masu hada maganin suka yi yanzu, lamarin da ya sa mutane suka fara sanin wane ne mai hada magani kuma ya wuce haka saboda shi yake gano maganin, ya hada shi ya kuma sarrafa shi,” inji shi.

Yayin da masu harhada magunguna ke qoqarin ganin al’umma sun fahimci muhimancin rawar da suke takawa wajen kiwon lafiyar dan Adam, an kwashe lokaci mai tsawo ana kai ruwa-rana a tsakanin hukumomi da qungiyar dillalan magunguna.

Alhaji Hussaini Labaran Zakari Shugaban Reshen Jihar Kano na Qungiyar Dillalan Magunguna ta Qasa, ya ce sun fada cewa idan sun ba da labari mahukunta su kama su dauki mataki mai tsanani a kan masu tu’ammali da qwayoyi. Idan kuma su masu sayar da magunguna ne suka ga wata illa suka dauki mataki a kai mahukumta su goya musu baya.

Yanzu haka dai wani kamfani da hadin gwiwa da gwamnati na aikin gina sabuwar kasuwa ta masu hada-hadar magunguna zalla a Kano a wani mataki na sanya ido sosai a kan yadda suke tafiyar da harkokinsu don bai wa al’umma kariya.