An yi bikin tunawa da tsohon shugaban Kamaru Ahmadu Ahidjo

A makon jiyane wasu jama’a da suke rike da tarihi suka tuna da tsohonShugaban kasar Kamaru, Ahmadou Ahidjo Babatoura, wanda ya cika Shekaru 24 da rasuwa a birnin Senegal na kasar Dakar a ranar 30 ga watan Nuwamban 1989. Duk da cewa gwamnatin da take ci a yanzu ba ta shirya wani biki, ko kuma […]

An yi bikin tunawa da tsohon shugaban Kamaru Ahmadu Ahidjo

A makon jiyane wasu jama’a da suke rike da tarihi suka tuna da tsohon
Shugaban kasar Kamaru, Ahmadou Ahidjo Babatoura, wanda ya cika Shekaru 24 da rasuwa a birnin Senegal na kasar Dakar a ranar 30 ga watan Nuwamban 1989.
Duk da cewa gwamnatin da take ci a yanzu ba ta shirya wani biki, ko kuma ba da wata sanarwa game da rasuwarshi da kuma ire-iren ayyukan da ya yi a lokacin da yake kan mulki ba, amma wannan rana ta zame wa al’ummar Kamaru masamman ma masu shekaru daga 40 izuwa sama, rana da ta shiga cikin zukatansu, musamman wadanda suka dandana kamun ludayinsa ko kuma kusantar mukarrabansa.
Mafi yawan jama’ar da suke tunawa da shi a yau, da kuma irin ayyukan da ya yi na ci gaban kasa na kunshe ne a cikin jam’iyyun siyasar adawa.
A tsakanin  shekara ta 1972 zuwa 1982, Gwamnatin Ahidjo ta maida hankali akan batun bunkasa tattalin arziki, har ta kai ga Kamaru kasancewa a sahun kasashen da suka bunkasa a Nahiyar Afrika kudu da Sahara.
Gwamnatinsa ta kulla hulda da kasar Sin da wasu kasashen duniya masu tasowa, lamarin da ya kaita ga tsaida wani shirin irin ababan da za a aiwatar a cikin wa’adin ko wasu shekaru biyar.
A tsakanin wadannan shekaru ya kafa wasu kamfanoni da suka hada da na sarrafa farin karfe a birnin Edea da kamfanin tsince irin shinkafa da za a noma.
Su kuwa masu kuma adawa da shi har a yanzu na zargin shi da tafiyar da mulkin mallaka, inda duk wani wanda ya daga kai ana harbe shi, kawai ba tare da bata lokaci ba, al’amarin da ake zargin ya salwantar da rayukan mutane da dama.
Ita ma Gwamnati mai ci na ta kokarin sasantawa da iyalansa, domin a samu maido garwarsa gida, a yi masa jana’iza, kamar yadda ake yi wa kowane mai amtsayi irin nasa.