An yi canjaras tsakanin Liverpool da Manchester United
Liverpool na ci gaba da jan ragamar teburin gasar da maki 46.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, ta yi kunnen doki da Manchester United a filin wasanta, na Anfield da ke Ingila.
An buga wasan hamayyar ne da yammacin ranar Lahadi, inda mutane da dama ke hasashen Liverpool za ta bai wa Manchester United kashi.
- Tinubu zai tafi Ghana rantsar da John Mahama
- ’Yan sanda sun kama matar da ta jefar da jaririnta a gefen hanya
Sai dai abun mamaki Man United, ta yi rawar gani a filin wasa na abokiyar hamayyarta.
Ɗan wasan bayan Manchester United, Lisandro Martinez ne, ya fara jefa ƙwallo a wasan a minti na 52.
A minti na 59 ne, ɗan wasan gaban Liverpool, Cody Gakpo, ya warware ƙwallon.
A minti na 70 Liverpool, ta jefa ƙwallo ta biyu ta hannun Mohamed Salah, a bugun fenareti bayan ƙwallo ta taɓa hannun De Ligt.
Bayan wasa ya kai minti 80, wato saura minti 10 kacal ya ƙare, Amad Diallo ya jefa wa Manchester United ƙwallo ta biyu.
Hakan ne ya kawo ƙarshen wasan, inda Liverpool ke da ƙwallo, Manchester United ma haka.
Yanzu haka Liverpool ce ke jan ragamar teburin gasar Firimiyar Ingila da maki 46, yayin da Manchester United ke mataki 13 da maki 23.