An yi dogon dare…
Duk da matsayin da jihohin Arewacin kasar nan suka samu kawunansu a cikin shekaru goma sha shidan da suka shude, sa’ilin da al’amuransu suka shiga tabarbarewa, gwamnonin da hakkin haka ya rataya a wuyansu ba su tabuka ba, don daukar wani mataki, walau na gaggawa ko wanda aka tsara na musaman, don magancewa. Haka nan […]
Duk da matsayin da jihohin Arewacin kasar nan suka samu kawunansu a cikin shekaru goma sha shidan da suka shude, sa’ilin da al’amuransu suka shiga tabarbarewa, gwamnonin da hakkin haka ya rataya a wuyansu ba su tabuka ba, don daukar wani mataki, walau na gaggawa ko wanda aka tsara na musaman, don magancewa. Haka nan suna ji, suna gani aka yi ta fatattaka yankin Arewa, ana haddasa rigingimu da fitintinun da suka rarraba kawunansu, aka kuma janyo wata fitina wai ita Boko Haram wacce ta tayar da zaune tsaye.
A wancan lokacin gwamnonin Arewa sun zamanto tamkar wasu lusarai, sun kasa yin magana ko tsawatawa dangane da abubuwan da ke faruwa a yankinsu, hasali ma an sha yin zargin cewa da su ne ake hada baki, ana ba kungiyar Boko Haram cikakken goyon bayan da ya kai ta ga matsayin da ta buwayi kowa. Wasu na cewa wasu gwamnonin ne ma da kansu ke shugabancin kungiyar Boko Haram din, kuma hakan ne ya sa aka gagara kai ta kasa cikin dan kankanen lokaci.
To, amma inda aka fi ganin wallen gwamnonin Arewa da kuma shugabanninta, musamman ma wadanda suka shude, shi ne rashin tabukawarsu wajen kawarwa Arewar da matsalolin da suka karfafa koma-bayan tattalin arziki sakamakon durkushewar daukacin masana’antun da ke yankin, kuma hakan ne ya yi sanadiyyar rashin aikin yi ga matasa da magidanta, ya kuma haddasa bakin talauci da mayata ga sauran jama’a.
A makon da ya gabata gwamnoni 12 cikin 19 na jihohion Arewa, tare da mataimakan wasu guda bakwai sun hallara a Kaduna a karkashin shugabancin Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima sun taru don gano bakin zaren warware dukkan matsalolin da suka addabi yankin Arewacin kasar nan da kuma dabarun kawo karshen masifar da kungiyar Boko Haram ta haddasa.
Gwamna Shettima ya ji takaicin yadda wadanda a halin yanzu ke bugun kirji, suna tinkaho cewa su ne manya ko kuma shugabannin Arewa suka kasa ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin ciyar da Jihar Arewa gaba kamar yadda shugabannin farko suka assasa, aka kuma ga alfanun haka, aka ci gajiyarsu a kasa baki daya. A cewarsa babu wani korafi ko kukan-zuccin da gwamnonin yanzu za su iya nunawa game da haka, idan har aka yi la’akari da yadda Arewar ta komo a halin yanzu. Mafita daga haka shi ne turzawar da shugabanni da gwamnonin yanzu za su yi na sauke nauyin da jama’arsu suka tattaru, suka doddora musu, su kuma tashi haikan wajen biya musu bukatunsu, ba biye wa son zukatansu ko ra’ayoyin wasu can daban ba.
A kowane zubin shugabannin jihohin Arewa, walau na soji ne ko kuma na farar hula, sai gwamnoninsu sun kirkiro wata dabi’a ko tsatsubar taro da sunan hada kan Arewa don amfanin jama’arta, kuma duk lokacin da aka yi taron babu wani abin alherin da za su tsinana wa jama’arsu, sai dai su ne za su amfana, domin tun can farko an tsiri taron ne don a kai ga biyan wata bukatar gwamnonin su kadai. Gwamnonin Arewa ne kadai ke yin irin wannan taron, suna kuma dodorido da sunan Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello, Firimiyan Jihar Arewa na farko, kuma na karshe, amma gwamnonin sauran jihohin sassan kasar nan ba su yi, ba su kuma tinkaho da firimiyoyin jihohin da suka gabata. To me ya sa sai a Arewa ne ake yawo da sunan Sardauna idan ana so a cuci talakawa?
A nan Arewaci gwamnoni sun sha yin irin wannan taron na yaudara, ana ta yi wa jama’a gafara-sa, amma har yanzu ba su ga kaho ba. Matakan magance matsalolin Arewa ba su bukatar yawan taron gwamnonin da suka zame tarin tsintsiya ba shara, domin gwamnonin suna da halin bin tafarkin da zai tserar da jama’arsu daga matsalolin da ke addabarsu nan take, domin su ne ke da wuka, su ne kuma ke da nama a hannuwansu. Idan har ba su yi amfani da dukiyar talakawan da aka danka masu amana ba wajen cire masu kangin talauci da fatara, to ina amfaninsu a gare su?
An sha jin cewa za a magance illolin barace-barace, da rashin aikin yin da ya zame ruwan dare a jihohin Arewa, amma duk a banza. Har yanzu jama’ar jihohin Arewar ce dai ke yawon bara a fadin tarayyar Najeriya, ana ta kyararsu duk inda suka kukkurda. Masana’antun Arewa kaf sun durkushe, an kuma yi watsi da aikin gona, jama’a na ta shiga bariki aikin ci-rani, wasu na faskaren itace, wasu na ga-ruwa, wasu na yankan farce, wasu na sayar da sukurdai ko bakin mai, wasu na yin dako da tura baro, wasu na sayar da jaridu, wasu kuma na gararamba a tituna, ba aiki sai ragaita ko zauna-gari-banza.
Jahilci da cututtuka sun fi yin katutu a Arewacin kasar nan, alhali kuwa dukiyar jihohin Arewa na da tarin yawa, kuma ba mai amfana daga gare ta sai azzaluman shugabanni da ‘yan barandarsu. Wai shin ma su wadancan sababbin gwamnonin da suke fafitukar farfado da martabar Arewar da magabatansu suka banzartar, za su kwatanta halaye irin na mazan jiya? Shin bayan hawansu mulki suna sane da cewa hatta magunguna a asibitoci ko kayayyakin fida babu, sai dai talakawa su yi ta bara a gidajen radiyo da talbijin kafin su samu dan abin da za a yi musu magani a asibitocin gwamnatocin da magabatansu suka karbi milyoyin Nairori don kulawa da lafiyar jama’arsu a banza? Baicin haka nan wace dabarar hadin gwiwa za su iya yi don tayar da masana’antun da suka duddurkushe da siradansu cikin kiftawa da bisimilla?
An dai sha ‘yan Arewa, kuma har yanzu ba su warke ba, amma sai dai sun kudurta aniyar cewa ba za su sake yarda gwamnoni da shugabanninsu su ci gaba da rarraba kawunansu, ko a yaudare su ba, domin an yi dogon dare, gari kuma ya waye.