An yi fada tsakanin magoya bayan Chelsea da na Manchester City a Ebonyi
Wasan da kulob din Chelsea da na Manchester City na Ingila suka yi a gasar rukunin firimiya na Ingila a ranar Lahadin da ta wuce ya kusa janyo asarar rayukan wasu matasa su uku a Abakaliki da ke Jihar Ebonyi.Wani labari da kafar labaran wasanni ta Allafrica.com ta kalato ya nuna yadda wadansu matasa uku […]

Wasan da kulob din Chelsea da na Manchester City na Ingila suka yi a gasar rukunin firimiya na Ingila a ranar Lahadin da ta wuce ya kusa janyo asarar rayukan wasu matasa su uku a Abakaliki da ke Jihar Ebonyi.
Wani labari da kafar labaran wasanni ta Allafrica.com ta kalato ya nuna yadda wadansu matasa uku suka samu mummunan rauni bayan sun kaure da fada a tsakaninsu.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa matasan sun yi cacar Naira dubu 40 ne a tsakaninsu watau magoya bayan kulob din Chelsea da kuma na Manchester City kafin a fara wasan. Kowannensu ya amince duk kulob din da ya samu nasara a wasan, to shi zai kwashi kudin. Kuma an yi wannan yarjejeniya ce a wani gidan kallon kwallo na Chidi Onyejegbu da ke Abakaliki na Jihar Ebonyi inda suka sanya manajan gidan kallon ya zama shaida.
Manajan ya ce mutumin da aka ba ajiyar kudin, mai goyon bayan kulob din Chelsea ne. A lokacin da wasa ya yi zafi kuma ya tabbatar kulob din Man City ya lallasa na Chelsesa da ci 3-0 kafin a tashi wasan sai ya sulale da kudin ya bar wurin. Daga nan sauran masu rufa masa baya suka rika sulalewa ba tare da sanin magoya bayan kulob din Man City ba al’amarin da ya sa ake zargin sun hada baki ne wurin sulalewar.
Jim kadan bayn an tashi daga wasan ne sai magoya bayan City suka nemi na Chelsea sama da kasa suka rasa, nan ne fa gardama ta sarke kuma fada ya kaure a tsakanin sauran magoya bayan kulob din Chelsea da kuma na Man City da ke wurin. An yi amfani da mugayen makamai da suka hada da kwalabe da adduna da sanduna wajen kai wa juna hari a lokacin fadan al’amarin da ya yi sanadiyyar jin rauni ga akalla mutum uku, biyu daga ciki magoya bayan Chelsea da kuma daya a bangaren masu goyon bayan kulob din Manchester City.
An garzaya da mutuanen da suka ji rauni zuwa wani asibiti mafi kusa sannan wani attajiri da ke wajen da abin ya faru ne ya mayar wa magoya bayan City kudinsu kafin a kashe wutar rikicin.
Manajan otel din da al’amarin ya faru a kan idonsa Chidi Onyejegbu ya ce bai kira ’yan sanda cikin al’amarin ba tun da an riga an sasanta.
Shi kuwa mutumin da ya gudu da kudin cacar ya bayyana cewa da gangan ya gudu bayan ya tabbatar an doke kulob din Chelsea.