An yi fim don tuna wa da marigayi Ibrahim B Nuhu

A makon jiya ne Kamfanin Nuhu Mobietone da fitaccen jarumi Ali Nuhu ya kafa ya kammala daukar fim din ‘Halacci’ a Abuja don tuna wa da furodusa marigayi Ibrahim B. Nuhu.Wata majiya da ke kusa da jarumin ta ce an sanya wa fim din sunan ‘Halacci’ ne saboda da irin ladabi da biyayya da kuma […]

An yi fim don tuna wa da marigayi Ibrahim B Nuhu
An yi fim don tuna wa da marigayi Ibrahim B Nuhu

A makon jiya ne Kamfanin Nuhu Mobietone da fitaccen jarumi Ali Nuhu ya kafa ya kammala daukar fim din ‘Halacci’ a Abuja don tuna wa da furodusa marigayi Ibrahim B. Nuhu.
Wata majiya da ke kusa da jarumin ta ce an sanya wa fim din sunan ‘Halacci’ ne saboda da irin ladabi da biyayya da kuma halaccin da marigayin ya nuna wa Ali Nuhu.
Fim din ‘Halacci’ labari ne a kan Aminullah (Ali Nuhu) da ke soyayya da Hidaya (Rahma Sadau), wacce take ’yar talakawa. Aminullah ya saya musu gida, ya saya mata mota, sannan ya ba ta Naira miliyan 30 don ta ja jari. Abin da bai sani ba shi ne, ashe ba son Allah da Annabi take yi masa ba, zuciyarta cike take da yaudara da kuma munafurci.
Kwatsam wata rana suna hira sai ta kalle shi ido-da-ido, sannan ta ce ba ta sonsa. A ranar da ya gane yaudararsa take sai ya shiga mawuyacin hali, aka rasa gane kansa, komai na duniya ya yi masa zafi.
Hakan ya sanya Nazir (Sadik Sani Sadik) kanen Aminullah ya yi alwashin dauka wa yayansa fansa, ya ce ba za ta ci bulus ba, dole sai ya rama wa yayansa. A nan aka fara dambarwa.
Ali Nuhu ne yaba da umarni, Jamil Nafseen ya tsara labarin, Musty Junior ya shirya shi.