An yi fyade 299 cikin wata 5 a Adamawa — Likita

Mutum 299 ne aka yi wa fyade a cikin wata biyar a daukacin jihar Adamawa. Manajar Cibiyar Kula da Wadanda aka Yi wa Fyade ta Jihar Adamawa, Dokta Usha Saxena, ta bayyana hakan ga manema labarai. Likitar ta nuna damuwarta game da yawaitar fyade a kan yara kanana da kuma ‘yan mata inda ta ce […]

An yi fyade 299 cikin wata 5 a Adamawa — Likita

Gwamna Umaru Fintiri na Jihar Adamawa

Mutum 299 ne aka yi wa fyade a cikin wata biyar a daukacin jihar Adamawa.

Manajar Cibiyar Kula da Wadanda aka Yi wa Fyade ta Jihar Adamawa, Dokta Usha Saxena, ta bayyana hakan ga manema labarai.

Likitar ta nuna damuwarta game da yawaitar fyade a kan yara kanana da kuma ‘yan mata inda ta ce a hakan ma yawancin iyaye na tsoron kai yara cibiyar kulawa da wadanda aka yi wa fyade saboda tsoron tsangwama.

“Iyaye da dama na tsoron kawo mana wadanda aka yi wa fyade saboda tsoron tsangwama a cikin al’umma ko kuma kyama”, inji ta.

Ta ce rashin wayar da kai kara a kan fyaden ne ke janyo yawaitar lamarin a jihar domin masu aikata laifukan ba sa tsoron abin da zai biyo baya.

“Sakacin iyaye na rashin kawo karar wanda ya aikata laifin ne yake sanya yara mata kanana kamuwa da cututtuka.

“Fyade na yawaita sosai a jihar Adamawa domin iyayen ba sa kawo karar masu aikata wannan aika-aika; hakan ke sanya masu laifin sake aikatawa ba tare da shakkar abin da zai biyo ba yaba”, inji ta.

A ”yan kwanakin nan dai batun fyade ya dauki hankali a Najeriya saboda yadda lamarin ke karuwa a sassa daban-daban na kasar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos