An yi gangamin goyon bayan tsohon Shugaban Masar a Kano

Dubban Musulmi a karkashin jagorancin kungiyar Jama’atu Tajdidil Islamiy ta Najeiya sun yi gangami don bayyana goyon bayansu ga tsohon Shugaban kasar Masar Muhammad Mursi da sojojin kasar suka tumbuke a makon jiya. Masu gangamin dauke da tutocin kasar Masar, sun gudanar da taron ne a Babban Masallacin Juma’a na cikin birnin Kano, inda suka […]

An yi gangamin goyon bayan tsohon Shugaban Masar a Kano
An yi gangamin goyon bayan tsohon Shugaban Masar a Kano

Dubban Musulmi a karkashin jagorancin kungiyar Jama’atu Tajdidil Islamiy ta Najeiya sun yi gangami don bayyana goyon bayansu ga tsohon Shugaban kasar Masar Muhammad Mursi da sojojin kasar suka tumbuke a makon jiya.
Masu gangamin dauke da tutocin kasar Masar, sun gudanar da taron ne a Babban Masallacin Juma’a na cikin birnin Kano, inda suka ce kifar da gwamnatin Mursi cin zali ne karara da kuma cin zarafin Musulunci da dimokuradiyya.
Shugaban kungiyar na kasa Malam Abubakar Mujahid, ya la’anci kasashen Amurka da Ingila da Faransa da Jamus, kan zarginsu da ingiza ’yan korensu na kasar Masar wajen yin juyin mulki ga halattacciyar gwamnati ta mafi rinjayen jama’ar Masar. “Ba wani abu ya sa ’yan koren kasashen Turai da sojoji yaran Yahudawa na kasar Masar suka kawar da gwamnatin Mursi ba, sai gani da suka yi ya saka dokokin Musulunci a cikin tsarin mulkin kasar, shi ya sa a yanzu suke shirin sake sauya kudin tsarin mulki saboda ba Musulunci suke so ba,” inji shi.
Ya ce sun shirya gangamin ne domin su bi sahun sauran Musulmi na kasashen Pakistan da Afghanistan da Turkiyya da Syria, wadanda suka yi zanga-zangar nuna kyama da la’antar juyin mulkin. Ya ce “Ba muna goyon bayan Mursi ne a karan kansa ba, sai dai muna goyon bayan gwamnatin Musulunci da yake kokarin kafawa a matsayinsa na halattaccen shugaban da ya ci zabe da yawan kuri’u mafiya rinjaye na jama’ar kasar Masar.”
Ya yaba kan matakin da Tarayyar Afirka (AU) ta dauka na dakatar da Masar daga kungiyar da kuma matsayin da Najeriya da kasashen Aljeriya da Maroko da Tunisiya suka dauka na rashin amincewa da gwamnatin Masar tare da bayyana ta da haramtacciya. Ya roki kasashen su ci gaba kan wannan matsayin da suka dauka.
Shugaban kungiyar na Jihar Kano, Malam Abdullahi Salihu Aukawa, ya yaba kan jajircewar ’yan kungiyar Ikhwanul Muslimina na kasar Masar wajen yin zaman dirshan tare da zanga-zanga har sai sun cimma burinsu na mayar da Mursi kan gadon mulki. Ya ce kin yarda da ’yan Ikhwan suka yi da karbar mukamai a cikin sabuwar gwamnatin ya nuna cewa ba mulki ne ya dame su ba, sai dai burinsu ne a tsayar da dokokin Musulunci, kamar yanda Mursi ya yi. Ya bukaci Musulmi su rika yi wa ’yan Ikhwanu addu’ar samun nasara.