An yi gangamin mubaya’a ga Buhari a Ibadan
A ranar Litinin din da ta wuce ne birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo, ya cika makil da dubban ‘yan Arewacin kasa da ke zaune a sashen Kudu maso Yamma, inda suka yi taro biyu a wurare daban-daban, domin yin mubaya’a ga dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyar APC, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya da mataimakinsa […]
A ranar Litinin din da ta wuce ne birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo, ya cika makil da dubban ‘yan Arewacin kasa da ke zaune a sashen Kudu maso Yamma, inda suka yi taro biyu a wurare daban-daban, domin yin mubaya’a ga dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyar APC, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo (SAN).
Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da kansa ya karbi bakuncin taron, wanda shi ne na farko da aka yi, a harabar ofishinsa, wanda Alhaji danladi Garba ya jagoranci jama’a, domin yin mubaya’a ga sake zaben Gwamna da Buhari a zabe mai zuwa. Gangamin taro na biyu da aka gudanar ne a cikin filin wasanni na Lekan Salami a karkashin Jagoran Kwamitin Yakin zaben Buhari na ‘yan Arewa, Sarkin Kudun Yamma, Alhaji Hassan Isiaka.
A jawabinsa, Gwamna Abiola Ajimobi, ya nuna farin cikinsa da mubaya’ar da ‘yan Arewa suka yi masa, wanda a nan take ya bayar da sanarwar nada daya daga cikinsu Alhaji Yahaya Ali a matsayin mai bai wa Gwamna shawara ta musamman a kan dangantakar al’ummar Hausawa da gwamnatin jihar, kuma ya sake tabbatar da cewa, gwamnatinsa ba za ta soke sana’ar ‘yan Okada a Jihar ba, domin suna gudanar da halastaccen aikin dogaro da kai da bunkasa tattalin arzikin jihar ne.
Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen tunatar da su illar da ke tattare da sayar da katin zabe na din din din, domin wannan kati shi ne abin dogaro, musamman idan suka yi amfani da shi wajen zaben Janar Muhammadu Buhari da shi kansa Gwamna Ajimobi a zabe mai zuwa, domin samar da canji mai dorewa.
Tun farko cikin jawabinsa Koodineton matasa ‘yan Arewa a Jihar Oyo, Alhaji danladi Garba, ya nuna matukar farin cikinsa da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a zamanin mulki Gwamna Ajimobi “wanda a wani lokaci can baya harkokin kasuwancinmu na masu sana’ar canjin kudi da dabbobi da kayan abinci a cikin kasuwanni da direbobi ya tsaya cik. Mun yi hasarar rayuka da miliyoyin kudi a wancan lokaci da babu batun tsaro a jihar sai a cikin shekaru hudu da suka gabata ne muka fara murmurewa, tare da kyautata zamantakewa a tsakaninmu da kabilun wannan jiha.
“Hakan ya samu ne a dalilin kyakkyawan jagoranci da Gwamna Ajimobi yake yi ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba,” inji shi.
A wajen gangamin da aka yi a filin wasanni na Lekan Salami kuwa, jawaban wakilan al’ummomin ‘yan Arewa mazauna jihohi shida na yammacin kasa sun fi mayar da hankali ne a kan tsame hannunsu daga batun mara wa Shugaba Goodluck Jonathan baya, da wasu mutane suka ari bakinsu domin ci musu albasa.
A jawabinsa, Jagoran Kwamitin yakin neman zaben Buhari na ‘yan Arewa a sashen Kudu maso Yamma, Sarkin Kudun Yamma, Alhaji Hassan Isiaka, ya shawarci jama’a su kasance masu girmama dokokin jihohin da suke zaune da kyautata zamantakewa a tsakaninsu da al’ummar garin da suke zaune.
Ya ce, “ziyarar da muka yi a baya domin ganawa da ‘yan uwanmu al’ummomin Fulani da Barebari da Nufawa da makamantansu da ke zaune a wannan sashe ta ba mu damar jiye wa kunnuwanmu irin matsalolin da suke fuskanta, wanda mukamin mai bayar da shawara da Gwamna Ajimobi ya bayar a Jihar Oyo, alamar share mana hawaye ce.
A nan, ya kamata mu fito da katunan zabe a hannayenmu a ranar zabe mu yi hakurin tsayuwar wannan rana mu jefa kuri’unmu ga Janara Muhammadu Buhari da dukkan ‘yan takarar mukamai daban-daban, domin samun canjin shugabanci mai adalci da zai amfani mulkin dimokuradiyya a Najeriya baki daya, amma ba irin salon mulkin PDP da ya jefa kasa cikin tabarbarewar tsaro da cin hanci da rashawa ba.