An yi garkuwa da babban jami’in Gwamnatin jihar Nasarawa

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga  ne sun yi garkuwa da babban sakatare a Ma’aikatar aiyukan gwamnatin jihar Nassarawa Jibrin Giza. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr Bola Longe,ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce maharan sun shiga gida Jibrin Giza da ke Lafiya babban birnin jihar Nassawara, da misalin karfe 12:30 na dare sannan […]

An yi garkuwa da babban jami’in Gwamnatin jihar Nasarawa

Jibrin Giza

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga  ne sun yi garkuwa da babban sakatare a Ma’aikatar aiyukan gwamnatin jihar Nassarawa Jibrin Giza.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr Bola Longe,ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce maharan sun shiga gida Jibrin Giza da ke Lafiya babban birnin jihar Nassawara, da misalin karfe 12:30 na dare sannan suka tafi da shi inda ba a sani ba.