An yi garkuwa da Basarake dan kasuwa a Katsina
Rahotanni na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da Dakacin Zandam Babangida Lawal a karamar hukumar Jibiya jihar Katsina. Bayan haka masu garkuwan sun yi awon gaba da wani dan kasuwan da ke garin Murtala Rabe, kamar yadda rahotannin suka sanar. Masu garkuwan sun shiga gidajen mutanen ne a […]
Rahotanni na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da Dakacin Zandam Babangida Lawal a karamar hukumar Jibiya jihar Katsina.
Bayan haka masu garkuwan sun yi awon gaba da wani dan kasuwan da ke garin Murtala Rabe, kamar yadda rahotannin suka sanar.
Masu garkuwan sun shiga gidajen mutanen ne a daren ranar Lahadi sai suka yi awon gaba da su. Akwai wasu makwabtan su da suka yi yunkurin kubutar da su amma hakan ya cutura suka samu raunuka.
Zuwa yanzu dai masu garkuwan basu sanar da kudin fansa ba