An yi garkuwa da daliban Jami’ar Tarayya da ke Lafia

Daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia da ke Jihar Nasarwa sun yi zanga-zanga bayan mahara sun sace abokan karatunsu a dakunan kwanansu

An yi garkuwa da daliban Jami’ar Tarayya da ke Lafia

Zanga-zangar sace daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia. (Hoto: Umar Mohammed)

’Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 1o na Jami’ar Tarayya ta Lafia da ke Jihar Nasarwa daga dakunan kwanansu.

Shaidu sun ce ’yan bindigar sun yi ta harbi babu kakkautawa suka yi awon gabad da daliban zuwan cikin daji daga dakunan kwanansu.

Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai wani hari da misalin karfe 2.30 na dare a dakunan kwanan dalibai na Conference Hotel a hanyar Makurdi suka sace wasu dalibai biyar.

Daga baya suka bulla a yankin Gandu da ke kallon jami’ar suna harbi, suka tisa keyar dalibai biyar, suka jikkata wasu da dama.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ’yan bindigar sun shafe kusan awa uku suna cin karensu babu babbaka ba tare da barazana daga jami’an tsaro ba.

Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’ar Tarraya ta Lafia, Abubakar Ibrahim, ya ce “yanzu ba za iya cewa ga hakikanin adadin daliban ba, saboda ba a cikin jami’ar dakunan kwanansu suke ba.

“Amma bayanan da muka samu sun nuna mutun uku zuwa biyar aka sace.

“Hukumar jami’ar na kokarin ganin duk dalibanta sun dawo kwana a cikin harabar makarantar,” in ji shi.

Sakamakon harin dai daliban jami’ar sun gudanar da zanga-zangar lumana ta neman a kawo karshe matsalar garkuwa da mutane da ta ki ci ta ki cinyewa a jami’ar.

Yawaitar garkuwa da dalibai a jami’ar ya sa dalibanta zama cikin fargaba.

A wannan zangon karatun kadai an sace dalibai sama da 15, sai da aka biya kudin fansa sannan aka sako su.

Wani dalibi da ’yan bindiga suka taba sacewa ya ce tun yamma ’yan bindigar suka tafiya da shi a daji a kafa, har sai da gari ya waye.

“Mu biyar suka kama ciki har da wata mace. Sun yi ta dukan mu, ga barazanar kisa, suka rika tafiya da mu, wani  lokaci ma har da guduwa a cikin dare.

“A karshe dai suka karbi kudin fansa N500,000 daga hannun iyayena kafin suka sako ni. Sauran ban san abin da ya faru da su ba, saboda ba za su iya biya ba,” in ji shi.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa