An yi garkuwa da dan shekara hudu a Abeokuta
Wasu mutane dauke da muggan makamai sun yi garkuwa da yaro dan shekara hudu mai suna Stephen a unguwar Oke Mosun, kusa da fadar Gwamnatin Jihar Ogun, a Abekuta. A cewar mahaifin yaron, Dokta Mucipay Kanu, yaron yana wasansa ne a harabar gidansu a yammancin Litinin da ta gabata, sai ya ji an kwankwasa kofa. […]
Wasu mutane dauke da muggan makamai sun yi garkuwa da yaro dan shekara hudu mai suna Stephen a unguwar Oke Mosun, kusa da fadar Gwamnatin Jihar Ogun, a Abekuta.
A cewar mahaifin yaron, Dokta Mucipay Kanu, yaron yana wasansa ne a harabar gidansu a yammancin Litinin da ta gabata, sai ya ji an kwankwasa kofa. Da ya je domin ya bude, nan take masu garkuwar suka yi awon gaba da shi, suka shiga wata motar tasi da suka ajiye a kofar gidan; wacce ba ta dauke da lamba. A lokacin da suke kokarin sulalewa da yaron, mutanen unguwar sun yi yunkurin far masu, da suka ga haka sai suka fara harbi a iska; abin da ya firgita jama’ar, kowa ya yi ta kansa har suka tafi da yaron.
Mukaddashin kakakin rudunar ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa tuni aka sanar da daukacin ‘yan sandan jihar kuma sun shirya tsaf domin ganin sun zakulo bata garin.