An yi garkuwa da gawa, ana neman Naira miliyan 1 a Ribas

Wasu ‘yan bindiga sun kwace wata gawa a garin Ahoada da ke karamar hukumar Ahoada ta Gabas a jihar Ribas, a jiya Jumu’a  ‘yan bindigar sun bukaci a biya Naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa. Wani ganau ya ce, ‘yan bindigar sun kwace gawar ne lokaci da wasu ‘yan uwan mamaci suka dauko shi […]

An yi garkuwa da gawa, ana neman Naira miliyan 1 a Ribas

Wasu ‘yan bindiga sun kwace wata gawa a garin Ahoada da ke karamar hukumar Ahoada ta Gabas a jihar Ribas, a jiya Jumu’a  ‘yan bindigar sun bukaci a biya Naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa.

Wani ganau ya ce, ‘yan bindigar sun kwace gawar ne lokaci da wasu ‘yan uwan mamaci suka dauko shi daga gida zuwa makabarta a hanyar su da ke Ahoeda, ‘yan bindigar sun dakatar da motar da ta dauko gawar daga nan su ka yi gaba da gawar.

‘Yan bindigar sun umarci direbar motar da ya sauka ya wuce, su kuma su ka shiga da gawar cikin daji.