An yi garkuwa da hadimin Yahaya Bello

Wurin da abin aka yi garkuwa da shi kusa yake da wani shingen binciken sojoji a kusa da gidan tsohon gwamnan Jihar Kogi

An yi garkuwa da hadimin Yahaya Bello

Yahaya Bello a kotu bayan Hukumar EFCC ta kama shi

’Yan ta’adda sun yi garkuwa da Honorabul Kabiru Onyene, sanannen hadimi ga tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Hon. Kabiru a ofishinsa da ke garin Okene da misalin karfe 7 na dare, bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Wani ganau ya ce “kwatsam muka jin harbe-harbe, jama’a sun fara guje-guje, shi ne muka gane cewa karar bindiga ne.

“Bayan ’yan mintoci sai muka ji harbe-harben a wurin ofishin Kabiru, inda suka tafi da shi.

“Amma abin mamaki shi ne wurin da abin ya faru kusa yake da wani shingen binciken sojoji a kusa da gidan tsohon gwamna,” in ji shi.

A safiyar Talata wani dan kabilarsa ya wallafa a kafar sada zumunta cewa, “A taya mu da addu’a, jiya da dare an yi garkuwa da dan uwana Honorabul Kabiru Onyene, daga ofishinsa.

“Allah (SWT) Ya kare shi Ya kuma yi wa hukumomi jagoranci su kubutar da shi da wuri domin ya dawo cikin iyalansa.”

Iyalan dan siyasan sun ce masu garkuwar ba su tuntube su ba, lamarin da ya kawo fargaba.

Mun tuntubi kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, game da lamarin amma ya ce ba shi da labari, sai dai ya bincika.

Sai dai kuma har zuwa lokacin da muka kammala wannan labari ba mu ji daga gare shi ba.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja