An yi garkuwa da jami’an Hukumar JAMB 4 a Kogi

An yi garkuwa da jami’an Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) su hudu a hanyar garin Lokoja zuwa da Obajana zuwa Kabba da ke jihar Kogi. Majiyarmu ta samu rahoton cewa, wadanda aka yi garkuwan da su ma’aikatan ofishin JAMB ne da ke Abuja. Lokacin da suke daidai garin Kabba […]

An yi garkuwa da jami’an Hukumar JAMB 4 a Kogi

Masu garkuwa da mutane

An yi garkuwa da jami’an Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) su hudu a hanyar garin Lokoja zuwa da Obajana zuwa Kabba da ke jihar Kogi.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, wadanda aka yi garkuwan da su ma’aikatan ofishin JAMB ne da ke Abuja. Lokacin da suke daidai garin Kabba ranar Lahadi da yamma don gudanar da shirin jarabawar dalibai.

‘Yan bindigar da ake zargin masu garkuwa da mutane sun bude wa motar jami’ain JAMB wuta a garin Obajana.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP William Ayah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce a yanzu haka sun kubutar da mutunm daya da aka kama mai suna Hamza, yana asibiti ana yi masa jinya.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa