An yi garkuwa da jarirai 3 a asibitin jami’ar Kalaba
Wasu ‘yan fashi da makami da suka kai 10 a daren ranar Lahadi sun shiga sashin jarirai na asibitin koyarwa na jami’ar Kalaba (UCTH) jihar Kuros Riba inda suka dauke jarirai uku. Kafin tafiya da jariran sun yi wa ma’aikatan asibitin duka da masu juna biyu da kuma nas da suke aiki a asibibitin. Ma’aikatan […]
Wasu ‘yan fashi da makami da suka kai 10 a daren ranar Lahadi sun shiga sashin jarirai na asibitin koyarwa na jami’ar Kalaba (UCTH) jihar Kuros Riba inda suka dauke jarirai uku.
Kafin tafiya da jariran sun yi wa ma’aikatan asibitin duka da masu juna biyu da kuma nas da suke aiki a asibibitin.
Ma’aikatan asibitin da masu jinya sun ce, ‘yan fashin sun shiga asibitin ne fuskokinsu a rufe dauke da bindigogi.