An yi garkuwa da Kansila na Jihar Nasarawa
A cewar majiyar iyalansa, tunda fari maharan sun yi nufin kashe Onumenya ne, amma daga bisani suka ƙyale shi bayan ya yi ta ba su haƙuri.
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Mohammed Onumenya, zaɓaɓɓen Kansila mai wakiltar mazaɓar Doka a ƙaramar hukumar Doma ta Jihar Nasarawa.
Lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Fabrairu, 2026, a kan hanyar Doma zuwa ƙauyen Yelwa.
- An kashe manomi kan taƙaddama da makiyaya a Yobe
- Masallacin Al-Ahfad ya shirya buɗe baki tare da kiristoci a Gombe
A cewar majiyar iyalansa, tunda fari maharan sun yi nufin kashe Onumenya ne, amma daga bisani suka ƙyale shi bayan ya yi ta ba su haƙuri.
“A cewar masu garkuwan, an ba su kwangilar kashe shi ne, amma ya roƙe su, shi ya sa suka bar shi da ransa.”
“Masu garkuwan sun kira wayar salula domin tattaunawa kan kuɗin fansa, amma sai maganar ta yanke. Sun sake kira da rana, amma ba su ce uffan ba suka sake katse kiran.”
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa (2/ic PPRO), Yusuf Idi Sani, ya bayyana cewa rundunar ta ƙaddamar da aikin haɗin gwiwa da sojoji, jami’an DSS, ’yan banga da mahauta domin ceto Kansilan da aka sace.