An yi garkuwa da Kansiloli biyu a Katsina

An yi garkuwa da Kansiloli biyu na karamar hukumar Safana a jihar Katsina jiya Laraba. Kasilolin su ne:  Hussaini Wanzam daga sashen harkar kudi da kuma Bishir Dan Jikko na sashen ruwa da tsaftar muhalli. An dai yi garkuwa da Kansilolin ne lokacin da suka tashi daga aiki a hanyar su ta zuwa garin Batsari. […]

An yi garkuwa da Kansiloli biyu a Katsina

An yi garkuwa da Kansiloli biyu na karamar hukumar Safana a jihar Katsina jiya Laraba.

Kasilolin su ne:  Hussaini Wanzam daga sashen harkar kudi da kuma Bishir Dan Jikko na sashen ruwa da tsaftar muhalli. An dai yi garkuwa da Kansilolin ne lokacin da suka tashi daga aiki a hanyar su ta zuwa garin Batsari.

Wata majiya na bayyana cewa, ya zuwa yanzu masu garkuwan basu bayyana kudin fansa da suke bukata ba.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Gambo ya tabbatar da yin garkuwan da kansiloli ya kuma ce a yanzu haka hukumar ‘yan sandan na  bakin kokarinta na kubutar da Kansilolin.