An yi garkuwa da Kodinetan Hukumar Albashi ta Ƙasa a Zamfara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Kodinetan Hukumar Tsara Albashi ta Ƙasa a Jihar Zamfara, Alhaji Bashir Abara Gummi tare da wasu matafiya a kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau

An yi garkuwa da Kodinetan Hukumar Albashi ta Ƙasa a Zamfara

‘Yan bindiga

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Kodinetan Hukumar Tsara Albashi ta Ƙasa a Jihar Zamfara, Alhaji Bashir Abara Gummi tare da wasu matafiya a kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau.

’Yan ta’addan tare babbar hanyar ne a ranar Lahadi, inda suka yi abin gaba da matafiya da dama, ciki har da shi.

Wasu majiyoyi tsaro sun bayyana cewa a lokacin harin, ’yan ta’addan sun buɗe wa motocin da ke wucewa a hanyar wuta, ind suka kashe wasu mutum biyu kafin su yi awon gaba da Alhaji Bashir da sauran matafiyan.

Alhaji Bashir Abara Gummi ya faɗa a hannun ’yan ta’adda ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja aiki, a cewar wani jami’in hukumar.

Sai dai Babban Mai Binciken Kuɗi na Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Dan Maliki, ya tsallake rijiya da baya, bayan da ya samu tserewa a lokacin harin.

Wakikinmu ya gano cewa motarsa ta iso wajen be bayan da ’yan bindiga suka tare rukunin farko na motoci, amma ya yi sauri ya juya kuma ya tsere.