An yi garkuwa da likitoci 10 cikin watanni biyu a Enugu

Kungiyar likitocin ta ce wannan lamarin na kara jefa mambobinta cikin fargaba.

An yi garkuwa da likitoci 10 cikin watanni biyu a Enugu

Likitoci

Kungiyar Likitoci ta Kasa reshen Jihar Enugu, ta ce a cikin watanni biyu kacal, sama da likitoci 10 ne suka shiga cikin hali mara dadi a jihar da ya hadar da garkuwa da wasu daga cikinsu.

Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da kungiyar ta fitar bayan wani taro da ta gudanar a ranar Juma’a.

Takardar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar likitocin reshen Jihar Enugu, Dokta Celestine Ugwoke, da sakataren kungiyar Dr Sunday Okafor, ta ce ta damu matuka da yadda ake samun rashin tsaro a asibitoci da cibiyoyin lafiya da suke aiki, lamarin da ke kara jefa mambobin kungiyar cikin fargaba.

Kungiyar ta bayyana wasu matakai da ya kamata a dauka domin kare likitoci da ke aiki a jihar ciki har da buƙatar gwamnatin jihar ta gaggauta samar da jami’an tsaro masu ingantattun makamai a dukkan asibitoci da cibiyoyin lafiya.

Haka zalika, kungiyar ta yi kira ga shugabannin asibitocin jihar da su samar wa likitoci kebabbun dakunan hutawa, da kuma motocin marasa lafiya da za su ke dauko su, sannan su kuma maida su gida.

Kungiyar likitocin ta yi kira ga gwamnatin Jihar Enugu da sauran masu ruwa da tsaki da su sani cewa “za mu zuba ido mu tabbatar an bi abubuwan da muka bukata, domin inganta aikin mu.”

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan