An yi garkuwa da ma’aikatan kwaleji 8 da kashe 1 a Osun

Rahotanni na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan kwalejin fasaha ta jihar Osun da ke garin Esa-Oke a jiya Talata. Jami’in hulda da jama’a na Kwalejin, Mista Adewale Oyekanmi, ne ya sanar da hakan a wani tattauna wa da kamfanin Dillancin Labarai  NAN ya yi da shi  ta wayar sadarwa a […]

An yi garkuwa da ma’aikatan kwaleji 8 da kashe 1 a Osun

Rahotanni na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan kwalejin fasaha ta jihar Osun da ke garin Esa-Oke a jiya Talata.

Jami’in hulda da jama’a na Kwalejin, Mista Adewale Oyekanmi, ne ya sanar da hakan a wani tattauna wa da kamfanin Dillancin Labarai  NAN ya yi da shi  ta wayar sadarwa a Osogbo babban birnin jihar.

‘Yan bindigan sun kai kashe daya daga cikin wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da yake yunkurin tsere wa.