An yi garkuwa da ma’aikatan simintin Dangote
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatam kamfanin simintin Dangote bayan sun taso daga wurin aiki a Jihar Edo.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatam kamfanin simintin Dangote da ke yankin Okpella a Jihar Edo.
A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka tare motocin ma’aikatan kamfanin a hanyar komawa gida bayan sun tashi aiki, inda suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.
An ce an sace su ne daga wata babbar bas din daukar ma’aikatan kamfanin kuma zuwa yanzu ba a tantance yawan wadanda abin ya rutsa da su ba.
Majiyoyi sun tabbatar cewa lamarin ya faru ne a Okpella, yankin da masana’antar simintin Dangote yake a Karamar Hukumar Etsako ta a Yamma a jihar.
- Sojoji sun aika jagoran ’yan bindiga da wasu 3 lahira a Kaduna
- Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da fetur a ma’aikatun gwamnati
Wani shaida a yankin ya ce, “mun samu labarin garkuwa da ma’aikatan kamfanin simintin Dangote a cikin wata bas kirar Coaster, amma ba mu san ko mutum nawa aka sace ba.
Wakikinmu ya yi kokarin samun karin haske game da lamarin daga kakakin ’yan sanda na Jihar Edo, Chidi Nwabuzor, amma jami’in bai amsa sako da kiran wakilin namu ba.