An yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

’Yan bindiga sun sace mahaifiyar mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara

An yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Dauda Kahutu Rarara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.

An yi garkuwa da Hajiya Hakima Adamu ne a gidanta da yankin Kahutu a Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina.

Shaidu a kauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

“A kafa suka zo, ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin suka yi garkuwa da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba  a lokacin da suka memi ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kadai suka dauka.

“Babu wani yunkuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke dauke da su,” in ji wani mazaunin kauyen na Kahutu.

Ya ce, “Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa suka tako zuwa cikin kauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kubutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan kauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan cigaba sosai a garinmu,” in ji shi.

Kokarin wakilinmu na ji daga Rarara bai yi nasara ba domin bai amsa kiran wayar ba, har zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.