An yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin Super Eagles

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samson Siasia a jihar Bayelsa. Mahaifiyar tsohon kocin mai suna Misis Beauty Ogere Siasia, mai shekaru 76 an sace ta ne da misalin karfe 2 na tsakar daren yau Litinin a gidanta da ke unguwar Odoni a Karamar Hukumar Sagbama […]

An yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin Super Eagles

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samson Siasia a jihar Bayelsa.

Mahaifiyar tsohon kocin mai suna Misis Beauty Ogere Siasia, mai shekaru 76 an sace ta ne da misalin karfe 2 na tsakar daren yau Litinin a gidanta da ke unguwar Odoni a Karamar Hukumar Sagbama da ke jihar Bayelsa.

Wannan shi ne karo na biyu da ake yin garkuwa da mahaifiyar Kocin. A shekarar 2015 ‘yan bindigar suka yi garkuwa da ita, inda har sai da tayi kwanaki 12 kafin a sako ta daga hannun masu garkuwa.

Kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar SP Asinim Butswat, ya ce yanzu haka jami’an ‘yan sandan jihar na ci gaba da bincike a unguwar Odoni don kubutar da Misis Beauty Ogere Siasia.