An yi garkuwa da mai ciki a hanyar zuwa asibiti haihuwa

Mijin matar, ya ce ya samu saƙon WhatsApp da ke sanar da shi an yi garkuwa matarsa.

An yi garkuwa da mai ciki a hanyar zuwa asibiti haihuwa

Wata mace mai juna biyu (Tsohuwar ajiya)

An yi garkuwa da wata mai tsohon ciki mai suna Madam Ogunbunmi a hanyar zuwa haihuwa a asibiti a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Matar wadda aka ce za ta haihu ta bar gidanta da ke yankin Oke Lantoro zuwa babban asibitin jihar da ke Abeokuta ne aka yi garkuwa da ita a hanya.

Mijinta mai suna Ogunbunmi Lateef, ya ce ya samu saƙon WhatsApp daga wadanda suka sace ta suna sanar da shi cewa sun yi garkuwa matarsa.

Kakakin ’yan sandan jihar, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi cikakken bayani ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, a ranar Alhamis, ta ce, “Ogunbunmi Lateef na Oke Lantoro ya kawo rahoto cewa matarsa ​​mai juna biyu da za ta haihu, ta bar gida zuwa asibitin jihar da ke Ijaiye a Abeokuta.

“Ya samu saƙon WhatsApp da ke tabbatar da yin garkuwa da matarsa ​​daga wasu mutane ɗauke da makamai.”

Ogun na daga cikin jihohin da ke fama da yawaitar aikata laifuka a yankin Kudu maso Yamma.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda