An yi garkuwa da mai unguwa da mata 4 a Katsina
Shaidu sun bayyana cewa, maharan sun shigo ƙauyen ne sanye da kayan sojoji, inda suka wuce kai-tsaye zuwa gidan mai unguwar, bayan sun fara harbe-harbe.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mai unguwar ƙauyen Kogari da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina, Alhaji Bello Abdulkaɗir a yayin da yake jimamin rasuwar mai ɗakinsa.
Maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mata huɗu a yayin farmakin da suka kai ranar Talata, a lokacin da ake tsaka da Sallar Isha’i a ƙauyen.
Shaidu sun bayyana cewa, maharan sun shigo ƙauyen ne sanye da kayan sojoji, inda suka wuce kai-tsaye zuwa gidan mai unguwar, bayan sun fara harbe-harbe.
Mazauna yankin suna zargin ’yan ta’addan yaran wani ƙasurgumin jagoran ’yan bindiga ne da ke addabar yankunan Ƙaramar Hukumar Matazu ne, mai suna Muhammadu.
- Wata mata ta cinna wa mijinta da amayarsa da ’ya’ya 2 wuta da fetur
- Mutanen ƙauyen Katsina sun fatattaki ’yan bindiga da ƙarfin wuta
Rahotanni sun bayyana cewa Muhammadu ya sha barazanar hana manoma zuwa gonakinsu a yankin, har sai jami’an tsaro da gwamnati sun dawo masa da dabbobin da suka ƙwace a hannunsa.
Shaidu sun ce maharan sun shafe kimanin mintoci 45 suna cin karensu babu babbaka a ƙauyen Kogari, inda suka fasa shagunan cajin waya suka sace wayoyi da sauran kayayyaki masu daraja.
Sabon harin ya tilasta mazauna ƙauyen, musamman mata da ƙananan yara yin ƙaura, saboda fargabar abin da zai iya biyo baya, a yayin da jama’a ke roƙon gwamnati ta turo ƙarin jami’an tsaro a yankin wanda ke yawan fama da hare-hare.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Cikin tashin hankali muke rayuwa. Mutane ba sa iya barci cikin kwanciyar hankali, kuma ba sa iya zuwa gonakinsu.”
Bayan da wakilinmu ya tuntuɓi mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Katsina, DSP Sadiq Aliyu, jami’in ya shafa masa cewa zai ba shi amsa bayan binciko gaskiyar lamarin.
Hare-haren ’yan bindiga sun ƙaru a baya-bayan a yankunan Ƙaramar Hukumar Matazu da makwabtantabda sauran sassan jihar Katsina, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen neman gwamnatin jihar ta rushe yarjejeniyar sulhun da aka yi da ’yan ta’adda, tunda sun saɓa alƙawarin da aka yi da su.