An yi garkuwa da masu jego biyu  a Adamawa

Wadansu ’yan bindiga sun yi garkuwa da matan wani mai suna Alhaji Hussain da ’ya’yansu uku tare da raunata ’yan sanda hudu a Karamar Hukumar Ganye da ke Jihar Adamawa a safiyar Talatar da ta gabata. Rohotonni sun ce ’yan bindigar sun shiga gidan Alhaji Hussaini Ahmadu ne da ke kusa da makarantar Sakandaren Gwamnati […]

An yi garkuwa da masu jego biyu  a Adamawa
An yi garkuwa da masu jego biyu  a Adamawa

Wadansu ’yan bindiga sun yi garkuwa da matan wani mai suna Alhaji Hussain da ’ya’yansu uku tare da raunata ’yan sanda hudu a Karamar Hukumar Ganye da ke Jihar Adamawa a safiyar Talatar da ta gabata.

Rohotonni sun ce ’yan bindigar sun shiga gidan Alhaji Hussaini Ahmadu ne da ke kusa da makarantar Sakandaren Gwamnati da misalin karfe biyu na dare inda suka yi garkuwa da matansa biyu masu shayarwa tare da ’ya’yansa uku. Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce harbe-harben ne suka fargar da ’yan sandan da ke unguwar inda suka fara musayar harbi a tsakaninsu. Ya ce a  lokacin ne ’yan sanda hudu suka ji rauni. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin.

“A halin yanzu mun shirya ’yan sanda da dama wadanda suka bi bayan ’yan bindigar domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su,” inji shi.

Aminiya ta gano cewa Alhaji Hussaini ya taba tsira daga masu garkuwa bayan sun fara fada a tsakaninsu. Hakan ya sanya aka karfafa matakan tsaro a gidansa, su kuma ’yan bindiga saboda sun sha yunkurin kama shi ba su yi nasara ba ya sanya suka zo gidansa da ba su same shi ba sai suka yi garkuwa da iyalansa.