An yi garkuwa da mata a ranar da mijinta ya rasu
An yi awon gaba da matar mamacin da ’ya’yanta da surukarta da direbansu.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo Zakawanu Garuba bayan rasuwarsa da ’yan sa’o’i, a ranar Asabar.
Matar mamacin da ’ya’yanta uku da surukarta da direbansu na hanyarsu ta komawa gida Auchi gabanin isowar gawarsa domin jana’iza ne, ’yan bindigar suka tare su a hanya suka shige da su cikin jeji.
Sai dai maharan ba su tafi ba da mahaifiyar marigayi Zakawanu wanda ya rasu a wani asibiti a Abuja bayan fama da rashin lafiya.
Gwamnan Jihar Edo Godwin Obasekiy ya umarci Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta yi dukkan mai yiwuwa domin kubutar da iyalan mamacin.
Mai magana da yawunsa, Crusoe Osagie ya ce tuni Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tuntubi takwaransa na Jihar Kogi, yake kuma jagorantar aikin ceton.
Ya ce gwamnan ya kuma tabbatar da cewa ’yan sandan sun samu dukkan abin da suke bukata na kayan aiki domin bin sawun masu garkuwar da kuma kubutar da mutanen da suka sace”.