An yi garkuwa da mutum 3 a garin Dan Ali
Wasu gungun mahara da ake zaton barayin shanu tare da yin garkuwa da mutane sun kai hari garin Dan-Ali da ke Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina. Maharan sun shiga cikin garin da misalin karfe daya da rabi na darenTalatar nan. Shigar su garin ke da wuya sai suka ci gaba da yin harbe-harben bindigogi […]
Wasu gungun mahara da ake zaton barayin shanu tare da yin garkuwa da mutane sun kai hari garin Dan-Ali da ke Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
Maharan sun shiga cikin garin da misalin karfe daya da rabi na darenTalatar nan. Shigar su garin ke da wuya sai suka ci gaba da yin harbe-harben bindigogi ba kakkautawa,sannan suka tunkari gidajen Alhaji Musa da Alhaji Usman inda aka ce sun yi awon gaba da mutum uku da kuma kudade da wasu kayayyaki.
Kamar yadda rahotonni suka fito daga garin, maharan har suka gama babu wani jami’in tsaron da ya leka garin balle a kai musu dauki.
Babu dai asarar rayuka a wannan hari kamar yadda Aminiya ta samu labari.
Yawaitar sata tare da garkuwa da mutane da kuma kashe su a wasu lokuta kullum abin yana sake daukar sabon salo a Jihar Katsina wanda hakan ya sa Gwamna Aminu Bello Masari a ranar Juma’ar da ta gabata ya sanya wa dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar shanu ko garkuwa da mutane. Kazalika, Sakataren Gwamnatin jihar kuma Shugaban Kwamitin Tsaro Dokta Mustafa Inuwa ya zargi jami’an sojin da aka tura jihar don yakar batagarin da kin gudanar da aikinsu yadda ya dace.
Dokta Mustafa ya nuna rashin gamsuwarsa game da rawar da sojojin ke takawa a wani shirin da ya gabatar a gidan Rediyon Tarayya Abuja wanda kuma aka yada a sauran tashoshin da ke karkashin gidan rediyon da ke sauran jihohi. Zargin da Babban Jami’in rundunar sojojin ta Bataliya ta 17 da ke jihar ya musanta.
Yankin Karamar Hukumar Danmusa dai na daga cikin wuraren da ke fuskantar hare-hare. Har zuwa rubuta wannan rahoto babu wani bayanin da ya fito daga bangaren jami’an tsaron.