An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa, maharan waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun auka wa unguwannin biyu a daren Laraba, inda suka riƙa harbi ba ƙaƙƙautawa kafin su shiga gida-gida suna neman mutanen da za su kwashe.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

‘Yan bindiga

Aƙalla wasu mutane 43 mazauna yanki guda ne ake zargin ’yan bindiga sun yi garkuwa da su a wasu hare-hare na bai-ɗaya da suka kai a ƙauyukan Takatsaba da Tarah da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa, maharan waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun auka wa unguwannin biyu a daren Laraba, inda suka riƙa harbi ba ƙaƙƙautawa kafin su shiga gida-gida suna neman mutanen da za su kwashe.

Wani mazaunin ƙauyen Takatsaba, wanda ya nemi a sakaye sunansa saboda wasu daga cikin danginsa na cikin waɗanda aka sace, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, kuma sun shafe kusan sa’o’i guda suna ƙaddamar da harin.

A cewarsa, maharan sun kashe wani yaro ɗan shekara 10, ɗan gidan Abdullahi Ado, sannan suka yi garkuwa da mutum 32 daga gidaje bakwai daban-daban.

Ya bayyana cewa, waɗanda aka sace ɗin sun haɗa da: mutum tara daga gidan Mamman Dogo; mutum biyar daga iyalan Abdullahi Ado, wanda aka kashe masa ɗa ɗan shekara 10 a lokacin harin; matar Babban Limamin ƙauyen; mutum biyu daga gidan Mai Unguwa; marayu guda biyu daga iyalan marigayi Malam Sani; mambobi takwas na gidan Malam Abubakar, waɗanda suka haɗa da: matansa da ƙananan yaransa; da kuma mutum biyar daga gidan Amadu Siro.

Majiyar ta ƙara da cewa, har yanzu ba a san inda wasu mazauna yankin suke ba, domin da yawa sun tsere cikin daji a lokacin da ake tsaka da harin.

“Mutane sun tsere kowa ya kama gabansa yayin da suke ƙoƙarin ceton rayukansu. Har yanzu ba mu san inda kowa yake ba saboda ruɗanin da ya biyo bayan harin,” in ji shi.

Ya bayyana cewa, jami’an tsaro ba su iso don ba da agaji ba a lokacin da ake tsaka da harin.

“Jami’an tsaronmu suna iya ƙoƙarinsu don kare mu, amma a wannan karon ’yan bindigar sun yi musu kwantan ɓauna. Jami’an tsaron suna yankin ɓangaren yamma na ƙauyen, yayin da maharan kuma suka shigo ta ɓangaren Kudu maso Gabas, inda suka gudanar da harin sannan suka fice,” in ji shi.

Mazaunin yankin sun bayyana cewa kwana takwas da suka gabata ma an kai hari a ƙauyen, amma jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakar maharan.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya