An yi garkuwa da shugaban hukumar kashe gobara na Legas

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Daraktan riko na hukumar kashe gobara na jihar Legas , Rasaki Musibau tare da wasu mutum shida a hanyar Itoikin zuwa Epe da ke karamar hukumar  Ikosi-Ejirin a jihar. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Bala Elkana ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi. A cewar kakakin ‘yan sandan […]

An yi garkuwa da shugaban hukumar kashe gobara na Legas

Masu garkuwa da mutane

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Daraktan riko na hukumar kashe gobara na jihar Legas , Rasaki Musibau tare da wasu mutum shida a hanyar Itoikin zuwa Epe da ke karamar hukumar  Ikosi-Ejirin a jihar.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Bala Elkana ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi.

A cewar kakakin ‘yan sandan wadand aka yi garkuwan da su sun hada da: Rasaki Musibau, Mufutau Adam, Funmilayo Adelumo, Asiogu Martha, Lasisi Muka da wasu mutum biyu.

Bala Elkana, ya ce an dawo da wasu motoci yayin aukuwar lamarin wadanda suka hada: moto kirar Toyota Sienna, Toyota Corolla da mota kirar Jeep Opel.