An yi garkuwa da shugaban UBEC da ‘yarsa
Masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja a jiya da misalin karfe 3 na rana, sun yi garkuwa da shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta kasa (UBEC) Dakta Mohammed Mahmood Abubakar da ‘yarsa. Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya tabbatar da yin garkuwa da shugaban yayin ‘yan bindigar suka kashe […]
Masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja a jiya da misalin karfe 3 na rana, sun yi garkuwa da shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta kasa (UBEC) Dakta Mohammed Mahmood Abubakar da ‘yarsa.
Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya tabbatar da yin garkuwa da shugaban yayin ‘yan bindigar suka kashe direban da ke tuka motar.
‘Yan bindigar sun sanya kayan sarki na soji inda suka tare motoci biyu kirar Land Cruiser Jeep mai lamba 07E o4 FG da mota kirar Toyota Sienna mai lamba SLJ 465 TN an yi garkuwan ne a kauyen Kurmin Kare karamar hukumar Kachiya hanyar Kaduna zuwa Abuja.