An yi garkuwa da iyalan Kwamishina a Sakkwato
’Yan bindiga sun sace suruka da dan uwan Kwamishinan Matasa na Jihar Sakkwato, Bashir Gorau
’Yan bindiga sun yi garkuwa da suruka da kuma dan uwan Kwamishinan Matasa da Bunkasa Wasanni a Jihar Sakkwato, Bashir Gorau.
Kwamishinan ya sanar cewa, “Da misalin karfe 12:45 na safe ne ’yan bindiga suka kai hari gidanmu da ke Garin Gorau, Karamar Hukumar Goronyo suka tafi da matar babban yayanmu Alhaji Lawali Gorau da wani dan uwanmu Hassan Manya.
- Jiragen sama ke kai wa ’yan bindiga makamai —Fadar Shugaban Kasa
- Abin da mahaifina ya fada min a hannun ’yan bindiga —Dalibar da aka sako
“Allah Ya kiyaye ya kuma dawo mana da su lafiya, Amin; Muna bukatar addu’o’nku,” inji shi.
Ya shaida wa wakilinmu a waya cewa da zuwan maharan suka fara harbi babu kakkautawa.
Sai dai ya ce surukar tasa da dan uwan nasa kadai ne ’yan bindigar suka yi garkuwa da su a kauyen.
“Har yanzu muna jiran kiransu don sanin bukatunsu,” inji Kwamishinan.