An sace tsohon Shugaban Hukumar NYSC, Janar Tsiga

’Yan bindigar sun yi garkuwa da tsohon Janar din sojan ne cikin dare ranar Laraba a ƙauyensu, Tsiga.

An sace tsohon Shugaban Hukumar NYSC, Janar Tsiga

’Yan bindiga su yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), Manjo-Janar Maharazu Tsiga (ritaya).

Rahotanni daga mahaifarsa Jihar Katsina na cewa maharan sun yi garkuwa da Janar Tsiga ne a kafin wayewar garin Alhamis a kauyensu, Tsiga.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu ya sanar cewa maharan sun yi awon gaba da Janar Tsiga ne tare da wasu mutum 13.

Wani makwabcin Janar Tsiga ya ce da misalin karfe 12 maharan suka fara barin wuta a garin, inda suka nufi gidan Janar din, suka yi awon gaba da shi.

Ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun jima suna duka kofar gidan Janar Tsiga, wanda daga bisani ya fito da kansa, “suka tafi da shi shi kadai… Mutum ya fi dari suka kawo harin.”

Kwamishinan wanda ya yi zargin hadin baki a harin da aka kai sa’o’i kadan bayan zuwan Janar Tsiga ƙauyen nasu da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara, ya bayyana cewa mutum hudu daga cikin wadanda aka sacen sun kubuto.

Ya yi zargin hadin bakin masu yi wa ’yan bindiga leken asiri aka sace Janar Tsiga, domin a cewarsa, da rana ya shigo garin, da daddare kuma aka kai harin tare da sace shi.

Kwamishinan, wanda ya ce jami’an tsaro sun bazama domin ceto wadanda aka sacen, ya bayyana cewa Janar din ya je garin ne shi kadai tare da direbansa, amma wannan tsautsayi ya auka masa.

Duk da cewa garin Tsiga bai saba fama da matsalar ’yan bindiga ba, amma kwamishinan ya bayyana cewa sau uku a baya-bayan nan suna kai hari tare da yin garkuwa da mutane a garin.

Matsalar ta addabi Karamar Hukumar Kankara kamar wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Katsina.